✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wuta ta tashi a Kannywood

An hana Zango zuwa Kano Afakallah zai kai Baban Chinedu kotu kan kazafi Yadda lamarin ya faro A makon jiya ne jarumi Adam A. Zango…

  • An hana Zango zuwa Kano
  • Afakallah zai kai Baban Chinedu kotu kan kazafi

Yadda lamarin ya faro

A makon jiya ne jarumi Adam A. Zango ya sanya wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram, inda ya ce zai je Kano domin kallon fim din nan na Rahama Sadau mai suna Mati A Zazzau, wanda ake nunawa a gidan sinima na Film House.

Ana cikin haka sai ya sake wallafa wani bidiyon, inda ya ce ba zai samu zuwa Kanon ba, saboda za a kama shi.

Idan ba a manta ba, a watannin baya Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta yi wa jaruman Kannywood rajista, amma wadansu ba su yi rajistar ba, ciki har da Adam A. Zango wanda ya ce ya fice daga masana’antar.

Wadansu daga cikin jaruman Kannywood sun zargi Shugaban Hukumar, Malam Isma’ila Na’abba Afakallah da yin amfani da siyasa don cin mutuncinsu.

Darakta Falalu Dorayi ya ce ya kamata hukumar ta tabbatar da cewa dokokinta suna aiki a kan kowa amma ba a kan wadansu tsiraru ba. Kuma ya nemi hukumar ta bibiyi dokokin da suka kafa ta maimakon fakewa da dokokin tana kai wa ’yan adawa hari.

A cewar Dorayi hukumar ta yi amfani da siyasa ce kawai ta ci mutuncin Zango. “Idan har hukuma za ta hana wadansu ’yan fim ganawa da masoyansu saboda ba su yi rajista ba, to da tun farko ta hana a kalli fim din don mutanen da ke cikin fim din ba su yi rajista ba. Ni ina ganin yin kungiya ra’ayi ne mutum zai iya kin shiga kungiya idan bai gamsu da ayyukanta ba,” inji shi.

Shi ma jarumi Sharu Mustapha Naburiska ya ce akwai bukatar hukumar ta kara duba dokokinta domin samun masalaha, “Doka ta Alkur’ani ce kadai ba a taba ta, amma kowace irin doka in dai mutum ne ya yi ta, to za a iya sa takarda da biro a gyara ta,” inji shi.

Shi ma jarumi T.Y. Shaba ya ce babu dangantaka tsakanin yin rajista da kallon fim. “Abin da aka yi wa Zango cin fuska ne. Don haka muna kira ga wannann hukuma ta ji tsoron Allah,” inji shi.

Har ila yau ’yan fim din sun zargi Shugaban Hukumar Afakallah da cin dunduniyar duk wani dan fim da ke goyon bayan jam’iyyar adawa, inda a cewarsu a kwanakin baya Afakallah ya rufe gidan daukar hoto na miliyoyn Naira mallakar jarumi kuma mawaki Sani Danja da ke kan Titin Hospital Road bisa zargin cewa bai cika sharuddan bude gidan hoto a jihar ba, lamarin da jarumin ya musanta inda ya ce bai bude gidan hoton ba sai da ya samu dukkan takardun iznin yin haka.

Sun zargi Afakallah ne ganin cewa tunda aka kafa Hukumar Tace Fina-Finan ba ta taba rufe gidan daukar hoto a jihar ba sai a kan na jarumi Sani Danja.

Daga baya hukumar ta bude gidan hoton inda aka ci gaba da gudanar da aiki.

Ba mu hana Adamu Zango zuwa kallon fim Kano ba – Afakallah

Sai dai tun a baya Hukumar Tace Fina-Finan ta musanta zargin na ’yan fim a kanta inda ta ce ba ta bin siyasa a gudanar da ayyukanta ba, illa su ’yan fim din ne ba su son bin dokoki inda kuma ta sha alwashin sanya kafar wando daya da duk wanda ya yi wa dokokin hukumar karan-tsaye.

Da yake karin haske game da batun hana Adam Zango zuwa kallon fim din Mati A Zazzau, a ranar Lahadin da ta gabata Isma’ila Afakallah ya ce babu siyasa a wannnan magana sai kokarin ganin Adam Zango ya bi doka da oda.

“Ba hana Adamu zuwa kallon fim muka yi ba. Mun dai hana shi gudanar da taron masoyansa da ya yi niyyar yi saboda bai nemi izinin yin haka ba. Adamu ya wallafa a shafinsa cewa yana gayyatar gangamin masoyansa wanda har ya ce zai raba kyaututtuka, to mu a fahimtarmu wannan abu da Adamu zai yi ya zama taro, don haka muna da dokokinmu da suka bayyana cewa dole sai mutum ya nemi izini kafin ya gudanar da kowane irin taro. Adamu kuma bai nemi izini ba.”

Shugaban Hukumar ya kara nanata matsayinta cewa ba za ta saurara wa duk wanda ba ya ganin darajar mutanen Kano ba, “Duk wanda yake niyyar girmama mutanen Kano to dole ya bi dokokin jihar. Muna da dokokinmu. Duk mutumin da ya ce zai karya mana doka, to, mu ma ba za mu kyale shi ba. Duk mutumin da bai yarda cewa Kannywood ko kuma harkar fina-finai na Hausa hanya ce ta sadarwa wacce za ta haskaka addini da al’adar mutanen Kano ba, to, mun hakura da shi ko wane ne shi ko da kuwa kyamara ce ta haife shi.”

Baban Chinedu ya zargi Afakallah da ci kudin marayu

Jarumin barkwancin nan Haruna Yusuf wanda aka fi sani da Baban Chinedu ya zargi Shugaban Hukumar Tace Fina-Finan ne da yin sama-da-fadi da tallafin da Gwamnatin Jihar Kano ta bayar ga iyalan jarumin barkwancin nan marigayi Rabilu Musa Ibro a lokacin auren ’yarsa shekara biyu da suka gabata.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da Babban Chinedu wanda babban amini ne ga marigayi Ibro ya ce Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da tallafin kudi ga iyalan marigayi Ibro ta hannun Shugaba Afakallah sai dai Afakallah bai mika kudin ga iyalan marigayi Ibro ba, maimakon haka sai ya dure kudi a aljihunsa lamarin da ya janyo sai da aka sayar da gida sannan aka iya biyan kudin kayan dakin yarinyar. “Kasancewar an ji gwamnati za ta bayar da tallafin aka sayi kayan da aka karbo bashin kayan da ka sanya a dakin yarinyar da aka dauki tsawon lokaci Afakallah bai kawo kudin ba hakan ya sa aka sayar da gidan gadon iyalan na Ibro aka biya bashin har Naira dubu 700,” inji shi.

Baban Chinedu ya kara da cewa abin da ya fi bata ransu shi ne yadda Afakallah ya dauko wani hoton kayan daki ya sanya a shafinsa na sada zumunta yana nuna hoton a matsayin shaidar kayan dakin da Gwamnatin Jihar Kano ta tallafa wa iyalan na Ibro da shi. “Bayan Afakallah ya sanya hoton wasu kayan daki a shafinsa na Istagram a matsayin irin kayan dakin da gwamnatin ta saya wa amaryar, mutane sun yi ta zuwa gidanta don ganin kayan wanda kuma aka ga ba su ba ne. Sannan a wancan lokacin ya sanya a shafinsa cewa wai iyalan Ibro suna godiya ga gwamnati. Kin ga wannan ai yaudara ce.

Baban Chinedu ya ce “Mu mun tabbata Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayar da kudin saboda ya san da maganar. Amma daga baya sai ga shi ya zo ya ce wai Gwamna bai bayar ba kuma ya hana mu dama mu ga Gwamna. Wannan ya sa muka san cewa lallai Gwamnan ya bayar da kudin shi ya san yadda ya yi da su, amma ya tsaya yana ta yi mana kwana.”

A zantawar da Aminiya ta yi da dan uwan marigayi Ibro wato Adnan Musa Danlasan ya  ce a matsayinsa na wakilin iyalan marigayi Ibro, “Babu wanda ya ba ni kudi ko kayan daki a matsayin tallafin Gwamnatin Jihar Kano. Kuma babu wanda ya fada min cewa an bayar da tallafin gare mu ballantana na yi zargin an hana mu.”

Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Shugaban Hukumar Malam Isma’ila Afakallah kan zargin ya ci tura.

Afakallah zai je kotu?

Sai dai Aminiya ta ci karo da takardar kotu da ke nuni da cewa Afakallah ya kai Baban Chinedu kotu domin kare kansa bisa zarge-zargen da ya yi masa.

A shirye nake mu hadu a kotu – Baban Chinedu

Da Aminiya ta tuntubi Baban Chinedu kan yunkurin kai shi kotu kan wannan zargi da ya yi, ya ce har zuwa lokacin bai samu sammaci daga kotun ba duk da cewa a shirye yake ya tunkari kowane kalubale game da maganganunsa. “Duk maganganun da na fadi cewa Afakallah ya cinye kudin tallafin kayan dakin ’yar Ibro ban janye ba. Ina nan a kan bakana. Kuma a shiye nake in amsa kiran kotu duk lokacin da takardar ta same ni, saboda na san ina da hujjojina a kan maganganuna,” inji shi.