✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wuta ta yi barna a gini mai hawa 12 a Legas

Wani gini mai hawa 24 da ke tsakiyar kasuwa a birnin Legas an wayi gari yana ci da wuta, inda wadanda suke kusa da ginin…

Ginin mai hawa 12 da wuta ta kama a Legas. Wani gini mai hawa 24 da ke tsakiyar kasuwa a birnin Legas an wayi gari yana ci da wuta, inda wadanda suke kusa da ginin suka ce tun da misalin karfe 6:00 na safe suka ga ginin yana cin wuta kuma cikin kankanen lokaci ne masu kashe gobara suka halara suka yi ta kokarin sun shawo karfin wutar. 

Wutar wadda ta fara a hawa na farko duk da kokarin da masu kashe gobara ke yi ta kai hawa na hudu lokacin da wakilinmu ya bar wurin. Sai dai ba mu samu labarin asarar rai ba, amma dukiya mai yawa ta salwanta domin hawa na farko inda bankin Mainstream yake ya kone kurmus, kuma hawan ne ke dauke da dakunan ajiyar kayan wasu ’yan kasar waje, kuma ana jin dukiya ta biliyoyin Naira ce ta salwanta.
Ba a san musabbabin gobarar ba, sai dai da yawa wadanda ke makwabtaka ginin sun ta’allaka shi da wutar lantarki da ta yi bindiga a daya daga cikin shagunan da ke cikin ginin.
A lokacin da wakilin Aminiya yake wurin baya ga masu kashe gobarar akwai jami’an tsaro da suka kewaye wurin domin gudun kada zauna gari banza su yi amfani da wannan dama domin satar dukiyar jama’a.