✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar daji na ci gaba da barna a Australia

Ma’aikatan kwana-kwana da baki masu yawon bude ido a Australia na tserewa daga yankin Kudu maso Yammacin kasar sakamakon tsananin zafi a daidai lokacin da…

Ma’aikatan kwana-kwana da baki masu yawon bude ido a Australia na tserewa daga yankin Kudu maso Yammacin kasar sakamakon tsananin zafi a daidai lokacin da ake fama da ibtila’in wutar daji a kasar.

Mahukunta sun ce, kimanin mutane dubu 30 suka bukaci a tsirar da su daga yankin Gippsland, da ke Kudu maso Yammacin kasar.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara a yankin, Ben Rankin ya ce, yanayin zafin da yankin ke fuskanta ya wuce kima, abin da ke barazana ga lafiyar ’yan yawon bude ido da ma’aikatan kwana-kwana.

Sakamakon yadda wutar dajin ke kara bazuwa da kuma tsananin zafi da ta haifar, yanzu haka daruruwan jami’an kwana-kwana sun janye daga yankin na Gippsland da akalla kilomita dubu daya daga gobarar da ake danganta ta da canjin yanayi.

Kimanin kadada miliyan uku, wato kwatankwacin girman kasar Belgium ya kone kurmus a yankin a sanadiyar wannan gobara da ta hallaka mutane akalla 10.

Akalla mutane bakwai ne suka bata a sakamakon gobarar dajin da ke ci gaba da babbaka a jihar Noubelle-Galles da ke kudancin Bictoriya a yankin Kudu maso Gabashin kasar, kana rahotanni sun ce mutane 11 ne suka halaka tun bayan barkewar iftila’in gobarar a cikin watan Satumban bara, ciki har da wani jami’ain ’yan kwana kwana guda, baya ga salwantar dimbin kadarori da dukiyoyin jama’a.