✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya bukaci a kori Ministar Sufurin Jiragen Sama

Dan takarar Majalisar Tarayya a mazabar Birnin Kudu da Buji a Jihar Jigawa a karkashin tsohuwar Jam’iyyar CPC, Injiniya Magaji Da’u Aliyu, ya bukaci Shugaba…

 Injiniya Magaji Da’u AliyuDan takarar Majalisar Tarayya a mazabar Birnin Kudu da Buji a Jihar Jigawa a karkashin tsohuwar Jam’iyyar CPC, Injiniya Magaji Da’u Aliyu, ya bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya gaggauta korar Ministar Sufurin Jiragen Sama Misis Stella Adaeze Oduah saboda abin da ya ce ta aikata na nuna son kai da rashin adalci, wajen juyar da jirgin kasar Habasha daga sauka a filin jirgin sama na Kano zuwa Enugu.
Injiniya Magaji Da’u, ya bayyana haka ne a hirarsa da Aminiya inda ya ce ya yi kiran ne sakamakon bayanin da aka buga a wasu jaridun kasar nan cewa jirgin na kasar Habasha ya fara sauka a Enugu, a ranar 24 ga Agustan nan, alhali bayanai sun yi nuna cewa tun farko an shirya jirgin zai rika sauka ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, kafin a karkatar da akalarsa zuwa Enugu.
Ya ce bayanai sun nuna Kakakin Hukumar Filayen Jiragen Sama ta kasa Misa Yakubu Dati, ya tabbatar da shirin saukar jirgin a Enugu, kamar yadda Kakakin Ministar, Mista Joe Obi ya sanar. Sai dai Dati ya ce bai san da cewa tun farko an shirya jirgin zai rika sauka ne a Kano ba.
Injiniya Da’u ya ce ba tun yanzu ne Ministar ta fara yin kafar ungulu ga filin jirgin Kano ba, wajen kautar da akalar jiragen wasu kasashen waje duk da gyare-gyare da sake inganta filin jirgin na
Kano da aka yi.
Ya ce yin hakan zai kara tauye kimar fadar Shugaban kasa, kuma manyan Arewa da na Jihar Kano ba za su taba mantawa da wannan abin ba.