Da Dumi Dumi

Ya ce kada dan Majailisar Tarayya na Koko-Besse da Maiyama ya nemi tazarce

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Maiyama Alhaji Ibrahim Aliyu Maiyama ya ce, dan Majlisar Tarayya Aminu Musa Koko bai cancanta yaci gaba da wakiltar al’ummar kananan hukumomin Koko-Besse da Maiyama a majalisar ba.
Alhaji Ibrahim Maiyama ya bayyana haka ne ga manema labarai a garin Maiyama, inda ya ce ba wanda ya dace ya wakilci al’ummar k ananan hukumomin Koko-Besse da Maiyama a zabe mai zuwa sai Alhaji Umaru Salla Sambawa U.U.
Ya ce, tun daga ranar da aka zabi Aminu Musa Koko ya wakilce su ba wani abin a zo-a gani da ya samar wa al’ummar yankin daga Gwamnatin Tarayya ko daga wajensa.
Alhaji Ibrahim Aliyu ya ci gaba da cewa abin da ya sa suke son su jawo Alhaji Umaru Salla Sambawa ya wakilce su a Majalisar Tarayya shi ne shi gogaggen dan siyasa ne mai son ci gaban al’umma, saboda ya yi shugabancin karamar Hukumar Maiyama har sau biyu sun ga kamun ludayinsa da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin.
Shi ma da yake zantawa da manema labarai a kan lamarin Kantoma Yankin Mungadi, Sulaiman Bagudu Maiyama ya ce, in ban da Gwamna dakingari babu wani dan siyasa da ya kawo ci gaba a yankin irin Alhaji Umaru Sallah Sambawa daga 1999 zuwa yanzu. “Saboda ko rike shugabancin karamar Hukumar Maiyama da ya yi sau biyu ya yi ayyuka da al’ummar yankin suka ci gajiyarsu,” inji shi.

Share