Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ya ciji macijin da ya sare shi sun yi mutuwar kasko

Ya ciji macijin da ya sare shi sun yi mutuwar kasko

Mai unguwar kauyen Ajanwa a garin Santrampur Tehsil, ya ce wani mutum mai shekara 60 ya mutu sanadiyyar sarar maciji a birnin Badodara a Jihar Gujarat ta kasar Indiya.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da ta wuce, kauyen da abin ya faru ya nada nisan kilomita 120 daga Gujarat. Mutumin ya mutu ne bayan ya rama sarar da macijin ya yi masa kuma ya kashe macijin nan take, kamar yadda jami’an kauyen suka sanar a ranar Litinin da ta gabata.

ADVERTISEMENT

Mai unguwar, ya kara da cewa, “Tsohon mai suna Parbat Gala Baria, yana tsaye ne a kusa da wata motar daukar kaya, lokacin da ake zuba masara a cikin motar sai ga wani maciji ya fito, sauran mutanen da ke kusa da wurin duka suka tsere, Parbat ya ci gaba da tsayuwa a wajen da nufin ya kama maciji.”

Macijin ya sari Parbat, a hannu inda a nan take ya rama cizon da macijin ya yi masa sannan ya rufe shi da duka har sai da ya kashe macijin a matsayin ramuwar gayya.

ADVERTISEMENT

Daga nan aka yi gaggawar daukan Parbat, zuwa asibitin birnin Lunawada daga bisani aka wuce da shi zuwa babban asibitin Godhra, amma daga baya ya mutu a asibitin sakamakon dafin macijin, inji Mai unguwar Baria.

Jami’an ’yan sandan Ajanwa sun samu rahoton abin da ya faru game da Parbat Gala Baria.