Da Dumi Dumi

Ya dace a rika hukunta iyayen da ’ya’yansu ba sa zuwa makaranta?

A makon jiya ne aka fara batun hukunta duk iyayen da ’ya’yansu ba sa zuwa makaranta. Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin jama’a. Hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane kuma ga abin da suke fada:

Gaskiya ya kamata hukuma ta rika sanya ido tare da hukunta iyayen da ba sa tura ’ya’yansu makaranta. Domin mafiya yawan yaran da suke lalacewa kuma ake amfani da su wajen aikin daba da bangar siyasa, yaran da ba su da ilimi ne. Don haka duk irin matakin da gwamnati za ta dauka wajen magance wannan matsala ya yi daidai. Kuma ya kamata hukuma ta rika daukar nauyin yaran da iyayensu ba su da karfin tura su zuwa makaranta, saboda muhimmancin ilimi.”

Gwamnati ta sanya ido kan irin wadannan iyayen – Sahabi Maileda

Daga Hussaini Isah, Jos

Ya kamata jama’a su rika tura ’ya’yansu zuwa makaranta saboda makaranta ita ce ginshikin ci gaban rayuwa. Sai da iilmi mutum zai samu duk wani matsayi da yake nema a duniya. Don haka gaskiya ya dace gwamnati ta sanya ido tare da hukunta duk iyayen da ba sa tura ’ya’yansu zuwa makaranta.’’

ADVERTISEMENT

Ya dace a hukunta irin wadannan iyaye – Sa’adatu M. Hussain

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Game da batun ko ya dace a rika hukunta duk iyayen da suka ki sanya ’ya’yansu a makaranta, a ra’ayina ya dace gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki wajen hukunta irin wadannan iyaye da suka kin sanya ’ya’yansu a makaranta da ma wadanda suke cire ’ya’yan nasu, walau don yi musu aure idan mata ne, ko kuma su rika tura su yin wasu sana’o’in da ba su dace ba, idan maza ne.

Misali, matasa ne ake tunanin za su ciyar da kowace al’umma gaba idan sun girma.  Idan kuwa haka ne, ta yaya za su iya shugabanci idan ba su yi ilimi ba. Ke nan nan gaba idan babu masu ilimi, za a samu jahilai ne masu yawa a al’umma kuma hakan ba zai haifar da da mai ido ba.”

Idan har gwamnati ta yi abin da ya dace ke nan – Aliyu Khalid

Daga Isiyaku Muhammed

Da farko dai yana da kyau mu fahimci ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Wanda idan mutum bai da shi to zai iya samun matsala a duk al’amuransa na zaman duniya. Duk da yake mutum bai san lokacin mutuwarsa ba, ya zama dole ne ya yi tanadi na zaman duniya mai tsawo. Ilimi na addini ko na zamani a kan same shi ne a gida ko makaranta, amma an fi sa ran samunsa a makaranta. Don haka zan iya goyon bayan duk wanda bai bar dansa ya je makaranta ba to ya cancanci ya fuskanci fushin hukuma. Amma zuwa makarantar ya kamata ne ya tsaya a matakin kananan makarantu, wato firamare zuwa karamar sakandare. Idan har gwmnati ta yi abin da ya dace, iyaye za su kara samun goyon baya saboda ba su son fuskantar fushin hukuma. Ya zama dai a makarantar yara za su iya karatu, rubutu har ma da lissafi. Kuma kafin wadannan dokoki su amsu wurin al’ummar kasa, akwai bukatar gwamnati ta mai da wannan karatun kyauta a kowace jiha. Ya zama kawai abin da ake bukata shi ne kasancewarsu a cikin aji su yi karatu. Kuma gwamnati ta ba da abubuwa da za su kwadaitar da iyayen da yaran. Idan muka duba a tarihi za mu ga irin dokar ce ta taimaki manyanmu na Arewa wadanda iyayensu ba su yarda su je karatun boko ba, amma daga baya sai ga shi su ne suke taimakon al’ummarsu.”

Kada a hukunta iyayen da suka ki kai yaransu makaranta – Maimuna Muhammad

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Ina ganin bai dace a ce za a rika hukunta iyayen da ba su kai ’ya’yansu makaranta ba, don ba a san dalilin da ya sanya suka yi hakan ba. Babu iyayen da ba sa so su ga ’ya’yansu sun samu ilimi, amma saboda halin yau, wadansu ko abincin yau ba su da shi, ballantana su samu sukunin sanya ’ya’yansu a makaranta. Kowa ya san halin karatu a yau sai kana da kudi, to mene ne dalilin da zai sa a hukunta iyayen da ba su da halin kai ’ya’yansu makaranta?

Kamata ya yi gwamnati ta rika bin hanyar lalama don ganin iyaye suna sanya ’ya’yansu a makaranta ba daukar matakin hukunci ba.”

Babu dalilin da zai hana yara zuwa makaranta yanzu – Nasiru Ibrahim (Nasi)

Daga Isiyaku Muhammed

A wannan lokaci da muke ciki kuma a wannan mulki na Shugaba Buhari ai an samu sauki da rangwame a bangaren ilimi, musamman a nan Jihar Kaduna. A nan Kaduna Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i ya mayar da makarantar firamare da karamar sakandare kyauta ake yi, sannan har babbar sakandarn kyauta ce ga mata. A firamare kuma ana ba yaran abinci da littafin rubutu da na karatu wasu lokuta, sannan a sakandare kuma a ba dalibai kayan makaranta. To da wannan saukin da ake ciki ai bai kamata a ce akwai yaran da ba sa zuwa makaranta ba, musamman makarantar firamare.”

Share