✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace ASUU ta jarraba tsarin IPPIS

A cikin makonnin nan ne Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sa zare da Gwamnatin Tarayya a kan umarnin da Shugaban Kasa ya bayar na…

A cikin makonnin nan ne Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sa zare da Gwamnatin Tarayya a kan umarnin da Shugaban Kasa ya bayar na kowace ma’aikar Gwamnatin Tarayya ta rika biyan albashi ma’aikatansu ta sabon tsari na bai-daya na biyan albashi dauke da bayanan ma’aikaci ta na’ura (IPPIS).  Shugaban Kasa Buhari ne ya bayar da wannan umarni tun ranar 8 ga Okutoban bana yayin da yake gabatar da kasafin kudin badi a gaban Majalisa Dokoki ta Kasa. Shugaba Buhari ya bayyana cewa kaddamar da tsarin zai taimaka wa gwamnati wajen toshe kafofin da ake amfani da su don zurarewar kudi daga lalitar gwamnati a daya daga cikin matakan da gwamnatinsa ke dauka wajen yaki da cin hanci da rashawa.

ASUU ta tsaya kai da fata cewa IPPIS tsarin biyan albashi ne da aka kirkiro don biyan ma’aikatan da suke aiki a ma’aikatu da hukumomin  Gwamnatin Tarayya (MDAs) wanda hakan ya saba wa tsarin dokar da ta samar da jami’o’i a kan masu ’yancin gashin kansu. Kuma ASUU ta kara da cewa wannan sabon tsari na IPPIS bai yi tanadi ba a kan biyan kudin ariyas na karin girma da alawus na karo karatu. Haka kuma ASUU ta yi zargin cewa an tsara IPPIS ne don yi wa farfesoshi wadanda za su yi ritaya in sun kai shekara 60 zagon kasa tunda yake sabon tsarin cewa ya yi sai shekarunsu sun kai 70 ne sannan za su iya yin ritaya. Don haka ne ma ASUU ta yi gargadin cewa ’ya’yanta za su yi wani yajin aiki idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakar musu albashinsu na watan Okutoban bana saboda kin amincewa da IPPIS.

A cikin wata sanarwa mai shafi 2 da ta fita a jaridar Daily Trust a ranar Talata, 22 ga Okutoban bana, Babban Akawu na Kasa Ahmed Idris ya yi watsi da abin da ya kira rashin fahimtar da ASUU ta yi wa tsarin IPPIS. Ya ce har yanzu shekarun ritayar farfesoshi suna nan a 70 su kuma sauran malaman jami’a za su yi ritaya ne a shekara 65. kamar yadda ya fada, malamin jami’ar da yake aikin kara kwarewa a wata jami’a za a biya shi kashi 50 na albashinsa a jami’ar da yake aikin. Sannan ya ci gaba da cewa malaman jami’ar da suka je aikin musaya a wasu jami’o’i, jami’ar da suke yin aikin za ta  biya su kashi 100 na albashinsu. Sannan daga baya jami’arsu ta asali za ta biya su albashi kashi 100 a cikin na wata 12 da suka dauka na zuwa aikin. Da yake magana a kan biyan alawus da tsarin IPPIS kuma cewa ya yi “Sauran alawus kuma wadanda aka amince a tsakanin kungiyar da gwamnati duk za a biya su kamar yadda aka tsara.” Ya ci gaba da cewa sabon tsarin biyan albashi na IPPIS ya taimaka wa gwamnati wajen samun rarar Naira biliyan 273 daga shekarar 2017 zuwa 2018.

Babban Akawun na Kasa ya ce an saka malaman  jami’ar ne a cikin wannan tsari na IPPIS tare da sanar da duk rassan kungiyoyinsu da suka hada da ASUU, yayin da sauran da suka hada da SSANU da NASU da kuma NAAT suka gamsu da tsarin na IPPIS, ASUU ce kawai take tantama da wannan tsari kamar yadda shugabanninta suka ambata kan hujjar cewa jami’o’i suna cin gashin kansu ne.

Idris ya ci gaba da cewa ma’aikatan wucin-gadi da masu yi wa kasa hidima (NYSC) da kuma masu aikin tuntuba ba ma’aikata ne na dindindin ba, don haka ba sa a cikin wannan tsari, abin da ya ce “Shi ne  ASUU take adawa da shi.” Ya ci gaba da cewa sauran kungiyoyin ma’aikatan jami’o’in tuni sun fara aiwatar da wannan shiri.

Mako daya kacal kafin lokacin da ASUU ta bayar don fara yajin aikin sai ta fitar da sanarwar janye yajin. Shugban ASUU, Biodun Agunyemi ya bayyana cewa ASUU ta janye yajin ne bayan da Shugaban Majalisar Dattawa ya roke ta. “Majalisar Dattawa ce ta shigo cikin batun,” inji shi.

Ganin yadda ASUU take da kima da yadda aka san ta da jajircewa a kan bin ka’ida, ’yan Najeriya da dama suna da yakinin cewa ASUU ba za ta ki amincewa da duk wani tsari don tabbatar da toshe hanyoyin da ake yi wa kasa zagon kasa ba wajen karkatar da kudaden gwamnati. Kudaden da kuma za a iya yin wasu ayyuka da dama da za su amfani jama’a.

Sanin cewa mai’aikaci  ba ya da bakin da zai zartar wa wanda ya ba shi aiki ta yadda zai biya shi, ASUU ta yi zargin cewa ’yancin da jami’o’i ke da shi ba zai samu tagomashi ba saboda yadda jami’o’in ba sa samar wa gwamnati haraji.  Don haka idan har sauran kungiyoyin ma’aikatan jami’a sun amince da wannan tsari na IPPIS, to ya kamata ita ma Kungiyar ASUU ta jarraba wannan sabon tsari don kada ya kasance wannan jayayya ta samar da wata dama wacce za ta sanya a rufe jami’o’in.