✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace gwamnati ta karbe kamfanin wutar lantarki daga hannun ’yan kasuwa?

Bayan da gwamnati ta sayar da kamfanin rarraba wutar lantarki ’yan kasuwa ake ta samun matsaloli a harkar samar da wutar lantarkin. Gwamnati tana kashe…

Bayan da gwamnati ta sayar da kamfanin rarraba wutar lantarki ’yan kasuwa ake ta samun matsaloli a harkar samar da wutar lantarkin. Gwamnati tana kashe makudan kudade a kan samar da wutar lantarki a kasar nan, amma har yanzu kamar gidan jiya ake, jama’a da dama suna ganin gara gwamnati ta karbe kamfanin daga hannun ’yan kasuwa watakila al’umma ta fi amfana daga wutar lantarkin.Wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin jama’a a kan haka:

Ya dace gwamnati ta karbe daga ‘yan kasuwa–Mohammadu Sani

Daga Bashir Lawal zakka, Birnin Kebbi

Eh, ya dace a karbe kamfanin wutar lantarki daga hannun ’yan kasuwa, saboda tun lokacin da kamfanin ya koma hannun ’yan kasuwa bayar da wutar lantarki ta tabarbare, kuma sai cuwa-cuwa ta karu a kamfanonin. Kuma duk lokacin da suka ga dama suka bushi iska sai kawai su kara kudin wuta fiye da misali, idan mutun ya yi magana sai su ce kamfani ne ba gwamnati ba. Kuma gwamnati ta ba su izini su sa wa kowa mita ’yar caji (Prepared meter) abin da ka sha shi za ka biya, amma sun ki saboda cuwa-cuwa. Ya kamata gwamnati ta karbe kamfanin.

Ya dace gwamnati ta kwace – Gide Musa Machika

Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina

Lallai yana da kyau gwamnati ta karbe batun bayar da wutar lantarki baki dayansa daga hannun ’yan kasuwa, bisa dalilin cewa, ba su biya wa jama’a bukatunsu yadda ya dace. An ce gaba dayan harkar wutar lantarki tana hannun kamfanoni, amma hidimar wutar tana hannun gwamnati. Sayen na’urar rarraba wutar, wayoyin da ake jan wutar tare da turakun da ake amfani da su don aza wayar da wani gyara in ya taso duk gwamnati ke yi maimakon su kamfanonin. Amma kuma da wata ya zo karshe sai ka ji an zo karbar kudi. Amma in gwamnati ta karba baki daya, to wadancan kudaden da take kashewa sai a juya su wani wurin a yi amfani da su.

Ya kamata ya zamanto yana hanun gwamnati – Habibu Abubakar

Daga Hussaini Isah, Jos

Gaskiyar al’amari ya kamata kamfanin wutar lantarki na kasa, ya zamanto yana hannun gwamnati. Domin lokacin da aka fitar da wannan kamfani daga hanun gwamnati, aka bai wa ’yan kasuwa dubban ’yan Najeriya da suke aiki a wajen sun rasa ayyukansu. Idan unguwarku akwai ma’aikacin wutar lantarki mutum daya, sai a yi wata biyu ba a dauke muku wuta ba. Amma da zarar kwana 28 sun cika, za su kawo maku takardar biyan kudin wutar da kuka sha.  Lokacin da kamfanin wutar lantarki ke hannun gwamnati ana samun wutar daidai gwargwado. Saboda haka idan gwamnati tana son, ta taimaka wa talakawan Najeriya, ta farfado da kamfanonin Najeriya ta sake dawo da kamfanin wutar lantarki na kasa zuwa hanunta. Domin ’yan kasuwa sun nuna cewa ba za su iya rike kamfani ba.

Ya kamata gwamanati ta amshe – Abubakar AATK

Daga Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina

To ai kullum abin sai kara lalacewa yake yi, don ba a san matsayin wutar  lantarki ba har yanzu. Da zarar an samu matsala a hannun mutane ake zuwa ana karbar kudin da za a yi gyara kuma daga su kamfanonin da ke bayar da wutar. Shin ina kudin da ake biyansu? A cikin wata da wuya ka samu wutar awa 2 zuwa 3 a lokaci guda, kuma sai a fi kwana biyar ba a ba ka wutar ba amma kuma sai a kawo maka bil na kwana 30 kuma ace ka biya. Amma idan a hannun gwamnati ne kamar yadda aka sani a baya, iya kudinka iya shagalinka. Kuma duk tsanani in an dauke wutar da wuya a yi minti 10 ba a maido ba. Tuni ya kamata a ce gwamnati ta amshe harkar wutar lantarkin.

Ya da ce gwamnati ta karbe kamfanin – Sani Adamu Kankara

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

A halin gaskiya gwamnati ta yi babban kuskure tun farko da ta damka wa ’yan kasuwa wannan babban kamfani wanda talaka ke karuwa da shi wajen neman abinci. A nawa ra’ayi ina goyon baya dari bisa dari gwamnati ta karbe dukiyar jama’a daga wadannan kamfanoni domin wahalar da talaka ke sha a kan wutar lantarki. Tunda kamfanin ya koma hannun ’yan kasuwa talakawa ke shan wahala, idan turken wutar lantarkinku ya lalace ko taransfoma ko iska ta yi muku barna ku za ku hada kudi ku sayo wadannan kayayyaki babu abin da kamfani zai yi muku. Amma lokacin da ke hannun gwamnati ba a samun irin wadannan matsaloli.

Gwamnati ta sake karbe kamfanin wutar lantarki – Salisu Mai Kananzir

Daga Hussaini Isah, Jos

Gaskiya ina goyon bayan gwamnati ta sake karbe kamfanin wutar lantarki daga hanun ’yan kasuwa. Domin idan gwamnati ta sake karbar kamfanin za a fi samun wutar lantarki a kasar nan.  Tun daga lokacin da ’yan kasuwa suka karbi wannan kamfani abubuwa suka lalace, ya zamanto ba a samun wutar lantarki a Najeriya. Yanzu idan wutar lantarki ta lalace a wasu wurare, dole sai gwamnati ta sanya hannu sannan a gyara. Kuma tun daga lokacin da wutar ta koma hannun ’yan kasuwa, suna rubuta kudaden wuta na son rai ne kaiwa su kai wa  masu amfani da wutar, idan ba a biya ba su yanke wutar. Don haka gwamnati ta sake karbe kamfanin daga hanun ’yan kasuwa shi ne mafita.