✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace kungiyoyin addini su ayyana wadanda za a zaba a mukamai?

Kasancewar zaben bana ya karato, da lura da yadda siyasar take zuwa. Wadansu malamai sun sanya baki a cikin lamarin har ake ganin ga inda…

Kasancewar zaben bana ya karato, da lura da yadda siyasar take zuwa. Wadansu malamai sun sanya baki a cikin lamarin har ake ganin ga inda suka dosa. Ga kuma yadda Kungizar Izala ta fito ta ce tana shawartar mabiyanta su zabi Shugaba Buhari domin ya maimaita. Hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin ra’yoyin mutane kan ko ya dace kungiyoyin addini su rika ayyana wadanda za a zaba, kuma ga amsar da suka fada:

 

Ya dace saboda su suke da ilimi – Muhammad Nasir

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Muhammad Nasir: “Malaman addni da kungiyoyin addini suna da ruwa-da-tsaki wajen nuna wa al’umma mutanen da ya kamata su zaba saboda su ne masua ilimi sun san mutanen da suke da nagartar da za su yi shugabanci. Yana da matukar muhimmanci malamai su haska wa talakwa mutanen da za a zaba, musamman a halin da muka samu kanmu a wannan lokaci. Idan da za a ce malamai su shiga siyasa to da za a rika samun sassauci domin da ba za a rika samun matsalolin da ake samu yanzu ba na sace-sacen kudin gwamnati da harkar bangar siyasa da sauransu.

 

Bai dace ba ko kadan -Sumayya Zubairu

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Sumayya Zaubairu: “Bai dace ba ko kadan malaman addini su rika sanya kansu cikin siyasa musamman wannan dimokuradiyyar. Kowa ya san suna da ra’ayi tunda mutane ne su amma ya fi dacewa su boye in lokaci ya yi su zabi wanda suke da ra’ayi ba sai sun fadi ba don kowace jam’iyya suna da mabiya a cikinta. Kamata ya yi su tafi da mabiyansu bai-daya, amma yin hakan zai tarwatsa hadin kansu ka ga tafiyar addini na iya samun cikas.”

 

Ya dace kungiyoyin addini su ayyana ’yan takarar – Musbahu Muhammad

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Musbahu Muhammad: “Hakika a ra’ayina malaman addini su ne suka fi dacewa  su fito su nuna wa jama’a ga dan takarar da ya cancanta su zaba. Dalilina shi ne a wajensu ne muke koyon addini bisa yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar. Idan muka yi karatun ta-natsu za mu iya fahimtar cewa duk wani dan takara da za ka zaba, Kur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) sun karantar da yadda ake zaben shugaba a Musulunci. Kuma a kan wannan fahimtar malaman Sunnah suke yada da’awarsu har kwanan gobe. A karshe ina so kowa ya natsu ya saurari wadannan malamai masu da’awar nuna wa mabiya ire-iren mutanen da ya kamata su zaba, zai gane cewa sun dogara ne kadai da koyarwar Alkur’ani da Hadisi wanda duk wani musulmi na kwarai ya yarda da haka. Kuma dimokuradiyya ta ba su damar bayyana ra’ayinsu a matsayinsu na ’yan kasa.”

 

Bai dace kungiyar addini ta ayyana dan takara ba – Tukur Bello

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Tukur Bello: “Gaskiya bai kamata kungiya mai jagorancin addini ta yi katsalanda a kan wani dan takara na siyasa musammam ma a ce ’yan takarar duk addininsu daya. Domin yin hakan yana kara tunzura mabiya wajen rarrabuwar kai. Bayan haka Najeriya kasa ce da Allah Ya wadatata da al’umma daban-daban, kasancewar haka ya sa kowa yana da ra’ayinsa. Amma babu damuwa idan malami a kan karan kansa ya ce shi a ra’ayinsa yana goyon bayan wani ba wai a ce ita kungiyar ba. Illar yin haka ya hada da samun nasara ga wanda ita kungiyar take kushewa. Mafi yawan malaman wallahi suna kare ra’ayinsu ne ba na al’umma ba, domin zai yi wuya ka ji kungiyar tana fafutikar nema wa mutane hakkinsu ga jagoran da take so domin akwai wata bukatarsu da ake biya. Daga karshe ina kira da babbar murya kungiyar addini ta daina yin katsalanda a kan abin da ba ta da iko a kansa domin siyasa sai dan siyasa addini kuma sai kungiyar addini.”

 

Gaskiya ya dace sosai su rika ayyanawa – Jamilu Sani Rarah

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Jamilu Sani: “Gaskiya ya dace sosai su rika ayyanawa domin su ne fitilar al’umma kuma su ne za su haska mutane su fahimci inda aka sa gaba. Bai kamata ana mayar da su baya a harkokin duniya ba. In kan Musulunci ne Annabi ya bayar da misali a lokacin da ya fada wa sahabinsa ba zai iya mulki ba, ka ga zabi ne wannan ya yi. Dawo kasa Sheikh Usman Dan Fodiyo su suka tafiyar da komai a zaben masu mulki. Don haka ya kamata a gane malamai fitila ce ta al’umma da ya kamata su rika fada musu wadanda ya kamata su zaba a kowane zabe domin mutane su zabi abin da ya fi daidai. Abdullahi Gwandu a littafansa Diya’us Siyasat da Diya’ul Hukkam, da Diya’ul Hulafa’i da Diya’uls -Sudan da Diya’ul Umara’i, duk a wadannan ya fadi yadda za a zabi shugaba, kuma da idan har wani bai dace a zabe shi ba, a fada, kuma komai da su ne muke kwaikwayo. Don haka na ga ya dace malaman addini su fada mana wadanda suka dace mu zaba da wadanda ba su dace mu zaba ba. In kuma suka fadi wanda suke ganin ya fi dacewa mu zaba bayan zabensa aka ga ya canja su fada mana wani sai mu canja.”

 

Bai dace kungiyoyin addini su rika sa baki a siyasa ba– Muhammad Sani Wudil

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Sani Wudil: “Gaskiya bai dace ba saboda a matsayinsu na malamai kamata ya yi su ba mutane shawara a kan halayen da za su yi la’akari da su wajen zaben mutane nagari amma ba kai-tsyae su ayyana wanda za a zaba ba. Yin hakan zai iya janyo zubewar kimarsu a wajen mutane domin za a dauka suna yin haka ne a matsayin yakin neman zabe saboda an ba su kudi da sauransu.”