✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace Shugaba Buhari ya sa baki a zaben shugabannin majalisa?

A yanzu hankali ya koma kan batun zaben shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai, inda wadansu da yawa suke ganin a wannan karon majaliar ta…

A yanzu hankali ya koma kan batun zaben shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai, inda wadansu da yawa suke ganin a wannan karon majaliar ta yi Shugaba Buhari zagon kasa wajen aiwatar da wasu ayyuka. Wannan ya sa suke tunanin ya kamata ya sanya baki wajen zaben shugabannin majalisar domin su taimaka masa wajen aiki. A daya bangaren kuma, wadansu suna ganin cewa kamata ya yi a bar ’yan majalisa su zabi shugabanninsu kamar yadda doka ta tanada. Wannan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane, kuma ga bin da suke cewa:

 

Ya kamata Shugaba Buhari ya nuna wadanda yake so – Musa Dan Malikin Kebbi

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

“Ya dace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna wa ’yan majalisa wadanda yake so su zaba a matsayin shugabanni idan yana son mulkinsa karo na biyu ya yi tasiri. Saboda idan bai sa baki ba, ko da ya so ya yi wa jama’a aiki ba zai samu goyon bayansu ba, iyaka za su yi ta yi masa kafar ungulu. Kowa ya ga irin yadda ta kasance tsakaninsa da shugabannin majalisar yanzu. Kowa ya ga irin rawar da suka taka wajen hana ci gaban kasar nan saboda wata bukata tasu, amma idan ya sa aka zabi shugabanni na kwarai duk dan Najeriya zai ga tasirin abin, za a ga ci gaba fiye da shekarun da suka gabata.”

 

Bai kamata ya saka baki ba – Kwamred Mukhtar

Daga Mohammed Yaba, Kaduna

“Bai kamata Buhari ya saka bakinsa wajen zaben wanda zai shugabaci majalisa ba kasancewar majalisa bangare ne mai zaman kansa. Don haka shawarata ita ce ya zura ido kawai ya ba su damar zaben wanda suke zo ya shugabance su hakan ne zai samar da kwanciyar hankali a majalisar.”

 

Ya dace ya tsoma baki – Alhaji Ibrahim Dan Talam Hadeja

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

“A gaskiya ya dace Buhari ya sa baki wajen zaben shugabanin majalisa don irin wannan ne ta sa a baya Shugaban Kasa Buhari ya samu matsala aka kasa samun hadin kai a tsakaninsa da ’yan majalisar, hakan ya sa ake ganin Gwamnatin Buhari ba ta yi wa talaka komai ba saboda wadanda aka zaba a matsayin shugabanni ba nasa ba ne.  Saboda haka a tawa shawara ya kamata Buhari ya tsoma baki a cikin maganar tunda dai bukatar maje Hajji, Sallah. Kuma bukatar ’yan Najeriya shi ne a yi wa talaka aiki kada a sake komawa gidan jiya. kowa ya sani Buhari mutum ne mai kishin talaka mai son a yi wa jama’a aiki amma saboda wadanda suka zama jagororin majalissar ba nasa ba ne, su ne suka yi ta cin dunduniyarsa suka hana ruwa gudu.”

 

Shugaba Buhari ya sanya baki saboda

gyara – Ahmed Abubakar Dutse

“Sa bakin Shugaba Buhari abu ne da ya dace ba don komai ba rashin saka bakinsa koma baya ne saboda a baya hakan ya sa ya samu matsala a mulkinsa. Saboda haka kamata ya yi domin kada a sake samun wata matsala irin ta baya Buhari ya sa baki ya dage ya ga an zabi shugabannin majalisa. Wadannan su ne abokan aikinsa su ne za su taimaka masa wajen yin abin da ya kamata na doka da ayyukan raya kasa da za su taimaki rayuwar talakawan da suka zabe shi.”

 

Ya dace ya sa baki – Alhaji Abubakar Muhammadu Atiku Walin Kalgo

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

“A nawa ra’ayin ya dace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya baki wajen zaben shugabannin majalisa saboda a shekarar 2015 da aka zabi Shugaba Buhari da ’yan majalisa, bai sa baki wajen zaben shugabannin majalisar ba. Rashin sanya bakinsa shi ya kawo ba a taba samun lalatacciyar majalisa irin ta wannan lokaci ba, saboda ko a wajen zaben ba a tsaya aka zabi shugabannin kwarai ba. Wannan shi ya sa ko da Shugaban Kasa ya tura wa majalisa kudiri na ci gaban kasa sai su yi fatali da shi, saboda babu shugabanci na kwarai.”

 

Ya dace Shugaba Buhari ya sanya baki – Malam Aliyu Sulaiman

Daga Mohammed Yaba, Kaduna

“Hakika ya dace Shugaba Buhari ya sa baki a zaben shugabannin majalisa ta tara domin kauce wa matsalar da ya samu da ’yan majalisa ta takwas wadanda shugabanninta ba sa tare yake da Buhari har ta kai ya samu cikas a aikinsa.”