✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace ’yan siyasa su fara batun zaben 2023 tun yanzu?

Wadansu ’yan siyasa tun kammala zaben bana suka fara buga kugen zaben 2023, alhali ba a gama hada hancin gwamnatocin da aka zaba a tarayya…

Wadansu ’yan siyasa tun kammala zaben bana suka fara buga kugen zaben 2023, alhali ba a gama hada hancin gwamnatocin da aka zaba a tarayya da jihohi ba. Wannan yana jawo cece-ku-ce a tsakanin jama’a inda wadansu ke ganin hakan ya yi wuri.

Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane a kan wannan lamari kamar haka:

 

Gaskiya akwai illa – Hon. Bashar Isa Matawalle

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya akwai illa sosai, domin ka ga akasarin ’yan siyasa sun taru a majalisa, ana maganar kasafin kudin  badi, wanda ake son a tabbatar da shi a cikin watan Disamba, kuma wannan aiki ne na ci gaban kasa da dole sai an yi kasa za ta samu ci gaba. Mutane hankalinsu zai juyo, ya koma kan harkar siyasa da zarar an fara batun zaben 2023, domin siyasa daukar hankali gare ta. Don haka wannan batu na a fara batun zaben 2023 a wannan lokaci ba ya da wani amfani. Domin da zarar an fara hakan gaba daya ’yan siyasa sun make kudi a mararsu, tunaninsu su samu nasara a zaben, kuma kudin da ya kamata a yi wa jama’a aiki da su, sai ka ga an koma buga hotunan ’yan takara da sayen motocin yakin neman zabe da sauransu. Saboda haka mu ajiye batun 2023 zuwa gaba, a yi wa al’ummar kasa ayyuka.

 

Ya yi wuri a fara yanzu –  Babawo Da’u

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

A gaskiya ya yi wuri domin yaushe ne ma aka gama zaben har shugabannin suka shiga ofis da wadansu za su fara batun zaben shekara uku nan gaba tun yanzu a bari sai lokaci ya yi. Talaka aikin raya kasa yake so daga wanda ya zaba ba gaggawar neman kujera ba idan ba a bai wa shugaba lokaci ba ta yaya zai fara aiki daga shigarsa wadansu su fara nuna sha’awarsu kan kujerar da yake kai?

A hakura a jira tunda akwai lokacin da hukumar zabe take bayarwa don nuna sha’awar takara.

 

A fara yanzu ya dace – Auwal Seiko

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

A nawa ra’ayin fara takara da wuri ya dace kuma ma, ai bai yi wuri ba tunda wannan gwamnati yanzu ta kai wata shida a karagar mulki.

Ko kasar Amurka da muke kwaikwayo a siyasa haka suke yi da zarar an kafa gwamnati nan take abokan hamayya suke daura damara ta fuskantar siyasar gaba mai zuwa.

Ba dalili ba ne a ce za a jira sai bayan wasu shekaru sannan masu neman takara su fara neman mukamai tun yanzu ya kamata kuma hakan daidai ne.

 

Babu laifi su fara – Ibrahim Abdulazeez (Dan Almajiri)

Daga Amina Abdullahi, Yola

Ita siyasa tamkar sharar gona ce tun kafin ruwa ya fara sauka ake share fage domin a tabbatar ta ina za a soma. Don haka a ganina ba laifi ba ne idan ’yan siyasa suka fara sharar fage na neman kujerun madafun iko na 2023 tun daga yanzu. Domin su san ta ina za su fara, shin kana ganin ya dace ka sake fitowa ko a’a, me ka yi wa al’ummarka? Amma abin lura shi ne kada wannan sharar fage na ’yan siyasa ya dauke hankalin wadanda suke rike da madafun mulki daga aiwatar da abubuwan da aka zabe su. Da ma matsalar da ake samu ita ce da an zo wannan lokaci an kai wannan gaba, musamman a wa’adi na biyu, za a ga hankali fa ya karkata wajen zaben da ke gaba tun lokaci bai yi ba.

 

Gaskiya babu amfani – Umar Yusuf

Daga Amina Abdullahi, Yola

A ra’ayina bai dace ba. Domin ya yi wuri kuma sabuwar gwamnatin da ta shigo ko shekara daya ba ta yi ba. Bai kamata ba domin alkawuran da gwamnatin yanzu ta dauka kafin a zabe ta ko rubu’insu ba ta riga ta cika ba. Kuma batun zaben 2023 ai na mai rai ne domin rayuwa ba tabbas. Idan kuma suka fara batun siyasa yanzu sun bata siyasar ke nan. Gaskiya babu amfani. Don Allah su kwantar da hankalinsu su jira lokaci.

 

Bai kamata ba – Umar Aliyu Abubakar

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Sam hakan bai kamata ba, dalili yaushe ma aka kammala zaben bana. Ka tuna fa akwai sauran kusan shekara 3 koma fiye da haka kafin zaben 2023. Gaskiya duk wani dan siyasa da ya fara batun zaben 2023 kamar bai san abin da yake ba. Ya kamata su maida hankali wajen yi wa al’umma aiki, ba batun zabe ba, domin mu talakawa mu ne masu zaben, to su bari mu ga abin da suka yi mana alkawari a zaben da ya gabata. Shawarata ga ’yan siyasa ita ce su tuna 2023 ta Allah ce, shin zai kai mu wannan lokaci ko a’a, don haka zu tsaya su yi wa kasa aiki, ba batun zaben 2023 ba.