✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya datse hannun yaro bisa zargin satar kifi

Wani mutum mai kiwon kifi ya datse hannun yaro dan shekaru 11 da ya yi zargin ya yi yunkurin sace masa kifi, inda ya yanke…

Wani mutum mai kiwon kifi ya datse hannun yaro dan shekaru 11 da ya yi zargin ya yi yunkurin sace masa kifi, inda ya yanke wa yaron dungulmin hannun sa da adda.

Mutumin mai shekaru 61 mai suna Jeremiah Obifor da ke zaune a yankin Ojo a Legas, ya shaida wa ‘yan sandan yankin cewa, barayi na zuwa satar masa kifin da yake kiwo lamarin da ya sa da yaga yaron dan shekara 11 mai suna Goodluck Amechi yana shawagi a inda yake kiwon sai ya dauka barawo ne, nan da nan ya sanya adda ya guntule masa hannun.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaidawa Aminiya cewa, rundunar na kan bincikar lamarin kafin a kai ga gurfanar da wanda ake zargin a kotu.