✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya jinjina wa al’ummar Jihar Oyo wajen karbar baki

Shugaban makarantar Ummul-Kitab da ke unguwar Sabo a birnin Ibadan, Ustaz Hafiz Usman, ya jinjina wa al’ummar Jihar Oyo kan karbar bakuncin jama’a (baki) da…

 Ustaz Hafiz Usman Shugaban makarantar Ummul-Kitab da ke unguwar Sabo a birnin Ibadan, Ustaz Hafiz Usman, ya jinjina wa al’ummar Jihar Oyo kan karbar bakuncin jama’a (baki) da suke yi da hannu biyu ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
Ustaz Hafiz ya bukaci sauran jihohi, musamman Jihar Plateau su yi koyi da wannan dabi’a, domin kasancewar baki a cakude da al’umma a ko’ina cikin duniya shi ne yake janyo bunkasar tattalin arziki da ci gaban ilmi na addini da na zamani.
Ustaz Hafiz ya yi wannan tsokaci ne a hirarsu da wakilinmu a Ibadan, inda ya ce, “A matsayina na haifaffen Jos, kuma dan asalin Jihar Plateau, amma zama ya kawo ni Ibadan, inda a dadadden nazarina na irin zamantakewar baki da ainihin ’yan asalin jihar ta Oyo, na fahimci mutane ne masu karbar baki da hannu bibbiyu, suna haba-haba da su ba tare da nuna kowane irin bambanci ba. Wannan dabi’a ta sanya ana samun ci gaban da kowa ke murna da shi, lamarin da ya sa nake fatan sauran jama’a, a wasu sassan kasar nan, musamman jihata, su yi koyi da ita.”
Malamin, wanda ya nuna alhininsa dangane da tabarbarewar zamantakewar jama’a a jihar ta Plateau, ya ce addinan Islam da kirista duk sun yi bayanan yadda za a yi kyakkyawar zamantakewa tsakanin al’umma, saboda haka ya kamata mu duba bayanan mu aiwatar da su don a sami ci gaba da zauna lafiya mai dorewa.
A wata fuskar kuma malamin ya nemi iyaye su tabbatar da yi wa ’ya’yansu kyakkyawar tarbiyya, su ba su ilmin addini da na zamani, wanda shi ne ginshikin kyautata rayuwar jama’a. Sannan ya bukaci miyagun ’yan siyasa, “Da suke amfani da ’ya’yanmu wajen tayar da zaune-tsaye domin cimma burinsu, su gyara tunaninsu. Su kuma mahukunta, su yi adalci cikin jagorancin da aka damka musu na jama’a. Su rika tuna cewa Allah Zai tambaye a gobe kiyama”. Inji shi.