✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a ce an kawo karshen matsalar Boko Haram –Ustaz Sarki

Usataz Muhammad Sarki shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Nasarawa. Kwanakin baya ya ziyarci tashar…

Ustaz Muhmmad SarkiUsataz Muhammad Sarki shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Nasarawa. Kwanakin baya ya ziyarci tashar talabijin ta Assunnah a Bauchi, kuma wakilinmu ya tattauna da shi kan matsalolin da Musulmi ke ciki a Najeriya, musamman matsalar Boko Haram:

Aminiya: Akaramakallah me za ka ce game da halin da ake ciki na rashin zaman lafiya a wasu jihohin Arewa?
Ustaz Sarki: Matsalolin da aka fada ciki a yanzu akwai bukatar kowa ya rika tunanin hanyar magance su. Duk mutumin da ba ya la’akari da haka a gaskiya ba ya da tunani, domin mai tunani idan ya hango matsala a nesa zai fara tunanin za ta iya matsowa inda yake. Don haka nake kira ga al’ummar Musulmi musamman na yankunan da wannan bala’i ke aukuwa kamar Jihar Borno da Yobe da Nasarawa da ke aukuwa a baya-baya, haka Jihar Adamawa inda bai dace a ce an sa ta cikin dokar ta-baci ba. Allah Yana kawo jarrabawa a lokacin da Musulmi suka yawaita laifuffuka domin ya zamo darasi ga masu kyakkyawar fahimta su koma ga Allah. Allah Madaukaki Yana cewa; “barna ta bayyana a tudu da koguna, saboda abin da mutane suke aikatawa, domin Allah Ya dandana musu sashin abin da suke yi (jarrabawa da masifa) ko hakan zai sa su tuba su dawo kan hanyar kwarai.”
A Najeriya Allah kadai Ya san laifuffukan da ake aikatawa, saboda akwai wuraren da suke miya da naman mutum akwai masu tsafi don yin kudi da mutum. Bala’o’i ga su nan ba su kirguwa kuma su ke sa Allah Ya kawo jarrabawa da bala’i domin hakan ya zame mana darasi don mu koma ga Allah. Ya zamo wajibi kowa ya yi wa kansa fada, kowa ya san laifin da yake aikatawa a boye da bayyane, idan kowa ya ji tsoron Allah, zai kawo sauki al’umma su samu rayuwar salama. Wadanda kuma ba wannan bala’i a wurinsu kowa ya matsa da rokon Allah da sanya malaman kirki cikin lamari don su taimaka da addu’a da lallashin jama’a a samu nasara Allah Ya kawar mana da wannan bala’i.
Abin da ya faru a Jihar Borno jim kadan da kaddamar da tashin Alhazai inda bala’in kashe-kashe ya biyo baya, abu ne mai ciwo. Gaskiya akwai bukatar mutane da gwamnati kowa ya zo mu fadada tunani. Akwai mutanen da ba a san suna mugun aiki ba, amma suna yi a boye domin abin da ke faruwa a yankin Arewa ke aukuwa, alhali a can baya lokacin da dan Arewa ke mulki wannan ba ya faruwa.
Abin tambaya ina ’yan Boko Haram suke samun makamai? Saboda harsashin da suke harbawa saye ake yi, kuma idan sun yi karo da jami’an tsaro za su yi asarar harsasan da bingigoginsu manya da kanana, to, ina suke samo wasu har yanzu ba su kare ba? Mai yiwuwa akwai wadanda suke da hannu da shuni ko wata dama a gwamnati suna tallafa musu don ganin ba a zauna lafiya ba. A wasu wurare akwai wadanda suka mayar da tashin hankali a matsayin samun nasara a lokacin zabe da makamantansu.
Aminiya: Wace hanya kake gani za a bi don kawo karshen matsalar Boko Haram?
Ustaz Sarki: Bai kamata a ce matsalar Boko Haram har yanzu tana nan a Najeriya ba, ya kamata a ce ta kare, gwamnati ta fadada tuni kan wannan lamari domin a kawo karshensa. Saboda wuraren da ake kai harin hatta sojojin da ya kamata a ce sun ba mu kariya, to su ma ba su tsira ba, yaya wannan abu zai zo karshe? Don haka muke gani kamar akwai wani munafunci cikin lamarin, kowa ya fadada tunaninsa da addu’a don Allah Ya nuna mana gaskiyar abin da ake boyewa.
Misali abin da ya faru a Nasarawa an kashe kusan ’yan sanda 90 cikin kayan aiki da SSS sun kai 10 amma har yanzu ba abin da aka yi kuma abin mamaki Daraktan SSS ya fito ya ce sun yafe musu, to, fisabilillahi yaya za a ce kasa ta zauna lafiya? Kuma lokacin da aka kashe wadannan jami’an tsaro ina bindigoginsu, anya ba wasu mutane ke haddasa wannan bala’i domin neman biyan bukatunsu ba? Don haka ina shawartar gwamnati da shugabanni a taimaka kada wani mutum ya fi karfin doka. Na ji dadin yadda majalisa take son fito da dokar da za ta iya kiran kowa gabanta duk wanda ya aikata laifi a yi masa magana, shi ne zai kawo ci gaba a samu zaman lafiya a kasa, mu fita daga wannan mummunan yanayi. Kuma masu rike da madafun iko ko Musulmi ne ko Kirista kowa ya yi imani aikin da yake yi Allah zai tambaye shi. Kuma kowa zai je gaban Allah ya amsa tambayoyin da za a yi masa idan ya aikata mai kyau ko mummuna. Don haka akwai bukatar mu fadada tunaninmu duk da cewa ni ba dan siyasa ba ne, abin da ke faruwa a Jam’iyyar PDP wani abu ne da ke nuna Shugaban Jam’iyya ya sauka da kuma Shugaban kasa kada ya tsaya takara. Duk hakan na faruwa ne saboda mutane suna gani ba a yi musu adalci, domin idan ana yi musu adalci ba za a kai ga haka ba.
A gefen talakawa, Allah Yana son talaka saboda ba wai Ya hana shi abin duniya saboda ba Ya sonsa ba ne, a’a wanda Allah Ya ba abin duniya idan da ya san matsalar da ake ciki shi ne zai fahimci ba a sonsa an dora masa nauyi mai yawa, Allah Yana son wanda yake cikin mawuyacin hali don Ya yafe masa zunubbansa, idan ka yi kokarin kuntata masa Allah Yana kallonka kuma zai iya daukar kowane mataki na hana ka sukuni kan mulkin ga kudi ga mulkin amma ka kasa zama lafiya.
Yanzu abin da ke faruwa a jami’o’i duk manya sun fitar da ’ya’yansu kasar waje amma na talakawa suna gida, masu mulki ba sa tunanin sauke hakkin talaka da ke kansu. Yaya za a kaunaci juna?  Kuma ya kamata ’yan Arewa su rike martabarsu don martabar kowa ta dawo, musamman mutanenmu da suke cikin gwamnati suna wasa da damarsu har su kare ba su taimaki mutanensu ba. Kuma duk irin matsayin da mutum ya hau ya sani dole a kwana a tashi zai bar wannan kujera. Don haka idan bai yi abin a zo a gani ba, haka zai kasance ya sauka a lalace.