✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata APC ta yi taka-tsantsan kan zaben shugabannin majalisa – Alhassan Doguwa

Dan Majalisar Wakilai Alhaji Alhassan Ado Doguwa da ke wakiltar mazabar Doguwa da Tudun Wada  a Jihar Kano, yana daya daga cikin wadanda suka fito…

Dan Majalisar Wakilai Alhaji Alhassan Ado Doguwa da ke wakiltar mazabar Doguwa da Tudun Wada  a Jihar Kano, yana daya daga cikin wadanda suka fito neman shugabancin majalisar. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa zai yi biyayya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari in ya kai ga burinsa.


Ganin Majalisar Wakilai mai wucewa, an yi ta samun damuwa tsakaninta da bangaren Shugaban Kasa, a matsayinka na wanda ya sake cin zabe, yaya kake ganin yadda wannan majalisa za ta kasance a wannan karo?

To, ina son in tabbatar maka cewa ina daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da mutumci da girman jam’iyyarmu ta APC a wannan majalisa. Kuma ina tabbatar maka cewa ina daga cikin mutanen da suka yi kokarin ganin an samu kyakyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Shugaba Buhari da wannan majalisa.

Domin a lokacin da aka yi kokarin zaben shugabannin majalisar ta 8, mu ne muka zabi shugabannin da jam’iyyarmu ta APC da Shugaban Kasa Buhari suka bayar da shawara a zaba, don a samu daidaito. Amma Allah cikin ikonsa aka samu wadansu daga cikinmu, suka hada baki da mutanen PDP aka zaba wa majalisa shugabancin da ba su ne jam’iyyarmu ta APC da Shugaba Buhari suka so a zaba ba.

Wannan tarnaki da aka samu da matsalolin da aka rika samu wajen gudanarwa, ya zama wajibi a wannan karo mu dauki mataki mu dunkule mu fito da shugabancin da zai taimaki Shugaban Kasa Muhammadu Bauhari.

 Mace ce gaskiyar maganar da ake yi cewa kana daga cikin wadanda suke son zama shugaban majalisar?

Babu shakka ina son in tabbatar da cewa tun daga lokacin da aka sake zabena, ina cikin wadanda suka fito takarar shugabancin wannan majalisa a wannan karo.

Kuma dalilina na fitowa takarar shugabancin majalisar shi ne na yarda zan bayar da kyakyawar gudunmawa, don a samu zaman lafiya da aiki cikin lumana da natsuwa da daidaito a tsakanin majalisa da bangaren Shugaba Kasa Buhari. Kuma na yarda a matsayina na dan Jam’iyyar APC, na fito daga jam’iyyar da take da rinjaye a wannan majalisa, wanda ya kamata a ba ta damar ta fitar da shugaban wannan majalisa. Kuma na fito daga yankin da duk Najeriya babu yankin da ya fi shi ba Jam’iyyar APC gudunmawa. Musamman wajen zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Sannan babu wani yanki da ya fi wannan yanki ’yan Majalisar Tarayya a Najeriya. Wannan yanki kuwa shi ne yankin Arewa maso Yamma.

Albarkacin wannan yanki da na fito, ina ganin na dace in zama shugaban wannan majalisa.

Ina son in tabbatar da cewa fitowata daga yankin da Mai girma Shugaban Kasa ya fito ba zai hana ni tsayawa takara ba. Domin tsarin mulkin kasar nan, bai hana wannan ba.

Bayan haka idan har jam’iyya a lokacin majalisar nan ta 8, ba ta ji kunyar tsayar da Femi Gbajabiamila ba daga Jihar Legas, yankin da Mataimakin Shugaban Kasa ya fito, duk da cewa ya samu akasi, ba na tsammanin akwai son zuciya ko abin kunya don ni da na fito daga Jihar Kano na nemi Shugaban Majalisar Wakilai tunda Shugaba Buhari ba daga Jihar Kano yake ba.

Bayan haka, a zauren majalisar nan a yau babu dan majalisar da ya girme ni, kan aikin majalisa da kuma dadewa a cikin majalisar.

Domin a yanzu a zango na 9 da wannan majalisa za ta shiga, zan shiga zango na 6 ne. Wannan ya ba ni damar da in magana ake yi ta gogewa da kwarewa da tsarin aikin majalisa babu wanda ya fi dacewa ya zama shugaban wannan majalisa irina.

Wannan ba na fada ba ne don na raina matsayin ’yan uwana sauran ’yan majalisa ba. Duk mutumin da ya zo majalisa idan ya yi shekara guda a cikinta, ya yi gogewar da zai iya zama komai. Hatta sababbin ’yan majalisa, doka ce kawai ta yi musu sarkakiya cewa ba za su iya zama ba.

Amma a cikin sababbin ’yan majalisa za a iya samun masu kwakwalwa da suka fi tawa. Za a iya samun masu ilimi da suka fi nawa, za a iya samun masu hikima da suka fi tawa. Amma doka ba ta ba su damar zama shugaban majalisa ba.

Saboda haka idan ana maganar dadewa a majalisa ne na cancanci zama shugaban majalisar. Amma ina son na tabbatar da cewa wannan yunkuri da nake yi da wannan dama da nake da ita, da fitowa da na yi neman shugaban majalisa, ina mai biyayya da girmama jam’iyya. Domin ita ce uwata ita ce alkiblata.

Idan yau jam’iyya ta zo da wani tsari da ya saba da bukatata zan ajiye bukatata in yi biyayya ga bukatar jam’iyya. Amma abin da ya kamata mu fada wa jam’iyya, shi ne ta yi taka-tsantsan duk abububuwan da za ta yi, ta tabbatar ta yi adalci ba son zuciya ba.

Domin duk matsalolin da ake samu wajen zabar shugabannin majalisa a Najeriya rashin adalci ne yake kawo su.

Abin da ya fi muni ma shi ne abin da ya faru wajen zaben shugabannin majalisa ta 8, aka zo aka samu wai Shugaban Majalisar Dattawa dan Jam’iyyar APC Mataimakinsa dan Jam’iyyar PDP.

Ba a taba yin irin wannan hadin gambiza ba,  sai wannan lokaci. Kuma duk wannan abin ya taso ne sakamakon rashin gaskiya da rashin adalci da jam’iyya ta shimfida wa kanta, karshe ’ya’yan jam’iyyar suka bijire mata.

Ni ban zabi Yakubu Dogara a matsayin Shugaban Majalisa ba. Mun yi abin da jam’iyya ta ce a yi ne. Mu kanmu mun sani abin da jam’iyya ta ce a yi bai yi kama da adalci ba. Shi ya sa ’yan majalisa suka bijire wa jam’iyya suka zabi Yakubu Dogara. Karshe haka muka yi shekara 4 nan kare jini biri jini, haka muka yi zama irin na doya da manja. Ba da hakkinmu ba, ’yan Najeriya suka rika kallonmu a matsayin masu tozarta Shugaban Kasa, suka rika kallonmu a matsayin mun bijire wa jam’iyya duk wadannan abubuwa sun faru ne a matsayin babu yadda za ka yi.

Amma duk da haka tun daga lokacin da muka fara aiki da Shugaba Buhari, har zuwa wannan lokaci, mun yarda Shugaba Buhari shugaba ne na kirki ingantacce, kuma mun yarda shugaba ne da jama’ar Najeriya suke kauna  kuma sun yarda sun damka amana a hanunsa. Wannan ya sa ko kana so ko ba ka so ya zama wajibi, in dai kai wakilin jama’a ne ka yi biyayya ga Shugaba Buhari. Kuma ka ba shi goyon baya ya samu nasara kan manufofinsa da akidunsa na tabbatar da gaskiya da yaki da cin hanci da rashawa da inganta harkar tsaro da kokarin canja tattalin arzikin Najeriya ya koma mai amfani ga al’ummar Najeriya baki daya.

Wannan ne ya sa muke tare da shi kuma muna ba da gudunmawa kan duk abin da yake yi.

Tunda Allah Ya taimake mu an sake zabarsa karo na biyu kuma ana magana ce ta alkibla kuma a ci gaba da wannan alkibla. To irinmu wadanda suka san daraja da mutuncin Shugaba Buhari a zauren majalisa ya zama wajibi a tasa mu a gaba mu shugabanci wannan majalisa domin ko babu komai a zauna lafiya, kuma a samu kyakyawan yanayi na aiki tsakanin Shugaban Kasa da majalisa.

In Shugaba Buhari ya same ni a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai, to ya je ya yi barci idonsa rufe, domin ya samu wanda zai rike masa amana da yi masa biyayya.

Karshe wane sako kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?

Ina  kira ga ’yan Najeriya mu yi wa Allah godiya kan yadda ya sake dawo mana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Domin dawowar Buhari ba karamar albarka ba ce Allah Ya yi mana.

Kuma muna rokon ’yan Najeriya su taya Shugaban Kasa da addu’a kuma mu yi wa kasa addu’a domin a zauna lafiya a samu dorewar tattalin arzikin Najeriya.

Irin barnar da Jam’iyyar PDP ta yi a kasar nan cikin shekara 16, ba zai yiwu Shugaba Buhari ya iya gyarawa cikin shekara 4 ba. Shekara 4 nan ma da aka kara masa ba zai iya gyarawa ba baki daya, amma na yarda zai dora kasar nan kan harsashin da za ta ci gaba.