✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Buhari ya kori manyan jami’an tsaron kasa – Kadariya Ahmed

Fitacciyar ‘yar jaridar nan Kadariya Ahmed ta bayyana cewa, babbar matsalar Najeriya a yanzu shi ne rashin tsaro dan haka kamata ya yi shugaba Buhari…

Fitacciyar ‘yar jaridar nan Kadariya Ahmed ta bayyana cewa, babbar matsalar Najeriya a yanzu shi ne rashin tsaro dan haka kamata ya yi shugaba Buhari ya kori manyan jami’an tsaron kasa, domin sun gaza tabuka komai.

Kadariya Ahmed, ta bayyana haka ne a zantawarta da Aminiya a yammacin yau Asabar a sa’ilin da ta   halarci taron da aka shirya a Legas domin bitar halin da kafafen yada labarai ke ciki da yadda ake tauye hakkin ‘yan jaridu da sauran al’ummar kasa.

A cewarwarta a yanzu kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram na kara karfi a yankunan Borno da Adamawa, “Kaga yanzu Boko Haram kara karfi suke, jihohin Borno, Yobe da Adamawa kullum cikin rigima ake, Jihata Zamfara a baya an fara samun sauki amma a yanzu masu satar mutane sun sake tasowa, haka ma a Kudancin kasar nan suma suna fama da tasu matsalar, dan haka tsaro shi ne babbar matsalar kasar nan a yanzu.” In ji ta.

Ta ce, ‘yan jarida da kafafen yada labarai a kasar nan na taka rawa wajen ruruta gaba da kabilanci a tsakanin al’ummar kasa ta yadda idan wani abu ya faru maimakon su maida hankali wajen gano matsalar da bada labari yadda yake sai su buge da zance dan kabila kaza ne ko kuma mai addini kaza ne, “Sai kaji ana Fulani ko Bayarabe ne, ko kuma musulmi ne ko kirista wannan salo ne na rarraba kan al’ummar kasa dan haka zai yi wuya al’umma su hada kan su waje guda su nemi ‘yancin su daga wajen mahukunta ko a fuskanci gwamnati da murya daya.” In ji ta.

Ta kara da cewa, a tsarin dimokuraddiya kamata ya yi a bai wa ‘yan kasa ‘yancin fitowa su bayyana ra’ayin su in anyi masu ba daidai ba, kana gwamnati ta dinga sauraren koken al’ummarta ba sai sun kai ga fitowa yin zanga-zanga ba.