✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Buhari ya sa ido kan ministocinsa – Goronyo

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ACPN ta Kasa Shiyyar Arewa, Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo, ya ce ya kamata Shugaban Kasa Muhammadu  Buhari ya sa ido sosai…

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ACPN ta Kasa Shiyyar Arewa, Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo, ya ce ya kamata Shugaban Kasa Muhammadu  Buhari ya sa ido sosai a kan ministocinsa gudun kada su ba shi kunya wajen sauke nauyin da aka dora musu. Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo ya yi wannan kira ne a zantawa da Aminiya a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce “Kada Shugaban Kasar ya rika katsalanda a aikin minista, ya barshi ya yi aikinsa ba sani ba sabo,  in minista ya bi doka ya tsira in ya taka kada a bar shi, ko shi wane ne a yi adalci ba maganar jam’iyya.”

Da ya juya kan maganar da Shugaba Buhari ya yi kan Kotun Sauraren Karar Zaben Shugaban Kasa cewa ya fi Atiku cancanta, ya ce a matsayinsa na dan adawa “Ra’ayi ne kowa da nasa, mutum bai kamata ya yabi kansa ba amma a zahirin gaskiya Buhari da Atiku shugabanni ne kuma kowa an ga abin da ya yi gwagwado, kan haka Buhari ya fi Atiku cancanta ina goyon bayan maganarsa a kotu.”

Mai Kassu ya yi tir da a ture ko farmakin da aka kai wa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu da wadansu ’ya’yan Kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biyafara suka kai masa a kasar Jamus. Ya ce ba wani dan Nijeriya da zai goyi bayan cin zarafin dan uwansa. Do haka abin da ’ya’yan kungiyar  suka yi bai dace ba.

Game da korafin wadansu ke yi cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ba ya aiki, ya ce a gaskiya ba ba ya aiki ba ne, a fahimtarsa Gwamna Tambuwal yana bin komai ne sannu a hankali gudun kada a maimaita abin da ya faru a zangon mulkinsa na farko, domin ya bai wa wadansu amana sun ci. “Don haka ne sai an duba wanda za a danka wa amanar al’umma ba ’yan tamore ba. Aminu Shugaba ne da ya tabbata Allah zai tambaye shi, ba haka kawai zai ki aiki a Sakkwato ba. Akwai abin da mu kanmu za mu yi la’akari duk mai son Gwamna ya rika hakuri adali ne ya dauki kowa daidai ba bambancin siyasa,” inji Mai Kassu.

Kan shirin da kananan jam’iyyu ke yi don tunkarar zaben shekarar 2023 kuwa, ya ce “Abu ne mai kyau ba a yi sauri ba kowa da kudirinsa, ba wata jam’iyya da za a ce mata karama domin kowace doka daya suke bi wajen samar da jam’iyya, karbuwa da cin zabe wannan na Allah ne.”