Da Dumi Dumi

Ya kamata gwamnati ta gina sinimomi na zamani don ceto Masana’antar Kannywood – Abdulkareem Papalaje

Abdulkareem Papalaje tare da Ali Nuhu
Abdulkareem Papalaje tare da Ali Nuhu

Abdulkareem Papalaje, sannannen marubucin fim ne a Masana’antar Kannywood, wanda ya  rubuta fina-finai masu yawa a tattaunawarsa da Aminiya ya bukaci gwamnati ta kafa sinimomi don ceto masana\antar.

Wane ne Papalaje?

Sunana Abdulkareem Ibrahim Khalid amma an fi sanina da Abdulkareem Papalaje, an haife ni a Bagauda a Karamar Hukumar Birnin Kano. Na yi makarantar firamare ta Gwagwarwa Special da ke a Birged, na yi sakandare ta Commercial da ke Kano daga nan sai na yi karatun share fagen shiga jami’a a CAS inda na samu shiga Jami’ar Bayero da ke Kano don yin nazarin Harshen Hausa. Tun ina firamare ni ma’abucin karance-karancen Hausa ne, nakan zo gaban allo in karanta wa ’yan ajinmu littattafan Hausa irin su Iliya Dan Maikarfi da sauransu. Kuma zan iya tunawa a lokacin ina sakandare duk wani abu da za a koyar da harshen Ingilishi ba na ganewa. Wannan ya sanya malamai da yawa suke jin haushina. Amma kuma wani abin mamaki na fi kowa cin darasin Hausa. Domin idan ma ana koya Hausa bana rubutu a littafi kuma da zaran malamin Hausar ya zo ya yi tambaya za ka ga ni ne nake amsawa. Don haka sai ya kasance shi kuma yana sona sosai.

Yaya ka tsinci kanka a matsayin marubucin fina-finai?

Na zama marubuci tun wajen shekarar 2002, akwai wani maigidana na farko mai suna Yaron Malam, (Allah Ya jikansa da rahama), ya taimake ni sosai. Domin na rubuta wajen littattafai uku amma ba ni da halin da zan buga su, kuma duk wani dillalin littafi da na tuntuba don ya taimaka ba wanda ya nuna sha’awarsa. To da yake Yaron Malam din dan Birged ne ni ma kuma haka, sai aka kafa wata kungiyar marubuta ta Birged wadda kuma ni ne Jami’in Watsa Labarai, Yaron Malam yakan halarci tarurrukanta. A nan ne ya ce zai taimaka ya buga labaran mutum hudu da aka zabi labaransu amma kowane daya daga cikinmu da aka zaba zai kawo Naira 4,000 shi kuma zai cika sauran kudin. Tunda yake a lokacin buga littafin bai wuce Naira dubu 25, ba.  Lokacin ba ni da ko Naira dubu daya, don haka sai na je na sayar da kayan kallona wato wani tsohon talabijin da yata ta yi aure ta bar mini da rikoda na hada kudin na kai masa. To bayan ya buga wannan littafi nawa mai suna Hantsi, sai ya sayar da shi cikin kankanen lokaci ya cire kudinsa ya ba ni nawa kaso wajen Naira dubu 17. Wannan littafi ya samu kasuwa kuma ni kaina ya sanya na fara yin suna duk inda na je sai in ga ana nuna ni.

ADVERTISEMENT

Bayan kora ta da aka yi daga Jami’ar Bayero saboda matsalar ban yi rajista da wuri ba, da na dawo gida da zama sai na fahimci ran mahaifina yana baci sosai a duk lokacin da ya gan ni zaune ba na zuwa makaranta. Saboda yana zaton rashin mayar da hankali ne ya haifar mini da haka. Duk kuwa da yake na yi masa bayanin yadda su Farfesa Dangambo da Farfesa Yusuf Adamu da sauransu suka yi bakin kokarinsu wajen ganin sun ba Baba Impossible hakuri a kan ya kyale mu bakwai da abin ya shafa ya ba mu dama mu yi rajista a lokacin amma ya ki.

Don haka daga karshe sai mahaifiyata ta umarce ni in koma wani gidanmu da ke Hotoro da zama. To lokacin da na koma abokina Ibrahim Birniwa shi tuni ya fara harkar rubutun fim, kuma idan yana rubutun ina kallon yadda yake yi. Wata rana na dawo sai na iske wadansu masu sana’ar hada fim ciki har da Nazifi Asananic suna tsaye a kofar gidan tare da ’yan sanda sun zo neman Birniwa a kan wai sun ba shi aikin rubutun fim ya yi musu kashi na 1 amma kuma ya ki ya gama musu na 2. Ka san dai halin masu aikin hannu. Ni kuma bayan na saurare su sai na ba su hakuri tare da daukar nauyin cewa zan sanya shi ya gama musu aikinsu cikin kwana  4, na kuma ba su tabbacin su dawo su karba bayan kwana hudun. Bayan sun tafi sai na kira Birniwa na fada masa abin da ya faru, shi kuma a lokacin ma ba ya Kano.

In takaita maka labari har bayan kwana biyu Ibrahim bai dawo ba, kuma bai aiko mini da aikin ba kamar yadda ya ce zai yi. Da na sake kiransa sai ya ce mini in rabu da su kawai. To ni kuma da yake na san alkawarin da na dauka sai na nemi izninsa na kama daga inda ya tsaya na ci gaba da rubutu, cikin kwana biyu na kammala na ba su. Suka karba suka ba ni ragowar cikon kudinsa wajen Naira dubu 20, wadanda su ne farkon kudin fim da na fara ci. Bayan sun je sun dauki fim din sai suka kira Birniwa suna yaba masa a kan yadda labarin ya dauki sabon salon da ya dace da ainihin abin da suke so.

Shi kuma bayan ya sake tambayarsu labari ya yi dai ko? Su kuma suka kara yabawa sosai. Daga nan kuma sai ya fada musu cewa to shi fa ba shi ne ya rubuta wannan karashen ba. Ya fada musu cewa ni ne na yi. To wannan shi ne farkon rubuta fim dina kuma shi ya jawo mini ayyuka na rubutun fim bayan da shi Birniwa ya tallata ni.

Yaya za ka kwatanta harkar rubutun fim lokacin da kuka fara zuwa yanzu?

A gaskiya ya fi daraja a wancan lokaci. Domin yanzu gaba daya ma ai kasuwar fim din ta fadi. Tunda yanzu ba wanda zai ba ka Naira dubu 100 ka rubuta masa fim.

Ana zargin marubuta fim da lalata tarbiyyar matasa musamman mata ganin irin yadda ake ta samun mata masu amfani da makamai a kan mazansu me za ka ce?

Ni a nawa ganin babu wata alaka a tsakanin fim da wadannan abubuwa da suke faruwa, tunda tun can asali ana samun irin wadannan abubuwa a kasar Hausa. Saboda kishin matanmu da rashin tarbiyya tun a gida. In dai kai ma’abocin zuwa kotu ne to ka san haka.

Zuwa yanzu wadanne fina-finai ka rubuta?

Na rubuta fina-finai da dama; akwai irinsu Adamsy da Madubin Dubawa duka na Ali Nuhu da Ni da Matata da Oga Abuja da sauransu.

Ka ce kasuwar fim ta fadi warwas, ina mafita?

A gaskiya mafita daya ce tal, domin mu marubuta sai masu shirya fina-finai sun samu ne za mu samu. Da farko ya kamata gwamnati ta sani akwai daruruwan matasa da ke cin abinci cikin wannan harka ta fim. Baya ga irin gudunmawar da ’yan fim din suka bayar wajen zabubbuka da kuma yadda suke kawo wa gwamnatoci haraji kama daga na biyan ofisoshinsu da sauransu. Don haka ya kamata a dube mu da idon basira a gina mana sinimomi na zamani, irin wadanda magidanci zai iya dauko iyalansa ya zo da su ciki su zauna su yi kallo ba tare da jimamin komai ba dangane da tsaro ko kuma tarbiyya. Irin sinimomin da ko ruwa ake yi ba ma za ka sani ba. Domin a farkon wannan harka ta irin haka ne masu shirya fina-finai suka rika bi gari-gari suna nuna sababbin fina-finan da suka fitar a sinimomi in sun gama hada kudinsu kuma sun samu riba sannan sai su sake shi a kasuwa.

A karshe wane kira za ka yi wa iyayen gidanka Ali Nuhu da Adam Zango ganin dangantaka ta dan yi tsami a tsakaninsu?

Ni ba abin da zan ce musu. Zan dai yi addu’a Allah Ya sa su fahimci juna. Amma dai zan ba wa magoya bayansu shawara ce, ya kamata su sani cewa duk irin son da za ka yi wa Ali Nuhu to Ali Nuhu kuwa ya fi son Adamu Zango a kanka. Haka  duk irin son da za ka nuna wa Adamu Zango, ina tabbatar maka cewa Adamun ya fi son Ali a kanka. Don haka kada ka shiga tsakanin wadannan mutane, don Allah ne kadai zai iya raba su, domin suna son junansu fiye da yadda duk mutum ke iya zato.

 

Share