✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata gwamnati ta taka wa ’yan kabilar Ibo birki – Shugaban Izala

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Inuwa dan’asabe ya bukaci Gwamnatin Tarayya da shugabannin ’yan kabilar Ibo su…

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Inuwa dan’asabe ya bukaci Gwamnatin Tarayya da shugabannin ’yan kabilar Ibo su taka wa wadansu daga cikin ’yan uwansu da ke neman musguna wa Hausawa da Fulani mazauna Kudu maso Gabas birki don dorewar zaman lafiya a kasar nan.
Alhaji Inuwa dan’asabe ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Masallacin Juma’a na Gwallaga da ke garin Bauchi.
Ya ce, “Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ba da dama ga duk dan Najeriya ya zauna a inda yake so ba tare da wani tsangwama ba, saboda haka babu wani dalili da zai sa a ce wasu kabilu su bar wani yankin na kasar nan.”
Shugaba na Izala ya kara da cewa: “Najeriya kasa daya ce kuma dole mu yi hakurin zama da juna domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali, duk inda aka zaga a yankin Arewa sai an samu ’yan kabilar Ibo yana harkokin kasuwancinsa, kamar sayar da magungunako kayan mota ba tare da tsangwama ba saboda mutanen Arewa ne gatan Ibo.”
Alhaji da’asabe ya ce babu addinin da ya kai Musulunci son zaman lafiya kuma duk inda aka samu Musulmi wanda yake da ilimin addini da na zamani mutum ne mai son zaman lafiya. “Don haka muna kira ga gwamnatocin jihohin kudancin kasar nan su shawarci matasan Ibo su daina neman tada zaune- tsaye, domin yin haka ba zai haifar musu da da mai ido ba,” inji shi.
Sai ya bukaci a ci gaba da addu’a ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ganin yadda aka samu zaman lafiya bayan ya karbi ragamar shugabancin kasar nan.