Search
Subscribe
‘Ya kamata gwamnati ta tallafa wa makarantu masu zaman kansu’

‘Ya kamata gwamnati ta tallafa wa makarantu masu zaman kansu’

Abukaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta rika ba makarantu masu zaman  kansu tallafi kamar yadda take bayarwa ga makarantunta domin su ci gaba da bayar da gudumawarsu ga ci gaban ilimi a jihar.

Wani lauya da ke Kwalijin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya Saminu  Abubakar ya yi kiran a wajen bikin raba kyatuttuka da yayen daliban Makarantar Umrabs karo na 15 da ya gudana a harabar makarantar da ke Hayin Dogo, Tudun Jukun Zariya.

Ya ce idan aka yi la’akari da gudumawar da makarantu masu zaman kansu ke bayarwa ta fannin ilimantar da ’ya’yan Jihar Kaduna tare da samar da aikin yi ga matasa, ya zama wajibi a nemi gwamnatin ta tallafa wa makarantu masu zaman kansu.

Da yake magana kan iyayen yara kuwa, ya bukaci su rubanya goyon bayan da suke bayarwa ga ci gaban makarantar domin ’ya’yansu ne ke amfana.

Hakimin Gundumar  Giwa Alhaji Abdulkarim Aminu ya shawarci al’ummar yankin da kada su yarda su bar damar da suka samu ta kubuce daga gare su na makarantar Umrabs, su taimaka mata iya karfinsu.

Basaraken ya shawarci iyayen yara su sanya ido tare da karfafa wa ’ya’yansu gwiwar yin karatu domin su ci gajiyarsu a gaba.

A jawabin Daraktan makarantar Malam Isa Sa’idu ya ce Makarantar Umrabs tana samun sakamako mai kyau duk da cewa har  yanzu hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ba ta fitar da sakamakon jarrabawa ba amma  a jarrabawar Hukumar JAMB daliban sun yi kwazo kwarai.

Malam Isa Sa’idu ya ce hukumar gudanarwar makarantar ta mayar da bangaren karatun Islamiyya ya zama dole ga dalibai bisa la’akari da wasu matsaloli daga daliban.

Ya tunatar da jama’a cewa akwai kwamitin kula da marayu na makarantar ga duk wanda ke da niyyar taimaka wa marayu yana iya zuwa makarantar domin neman bayani.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin