✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata kungiyoyin yankuna su zamo masu neman mafita ga kasa – Dansudu

Shugaban Kungiyar Kare Muradun ’Yan Arewa da ke zaune a Kudu (AUCF) Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu ya ce  Farfesa Ango Abdullahi ya yi kuskure kan…

Shugaban Kungiyar Kare Muradun ’Yan Arewa da ke zaune a Kudu (AUCF) Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu ya ce  Farfesa Ango Abdullahi ya yi kuskure kan bayanan da ya yi cewa Fulanin da ke zaune a Kudu su koma Arewa inda suka fito.

Alhaji Ado Dansudu ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a Legas, inda ya ce “Ba a kai lokacin da za a dauki irin wannan mataki ba tukuna. Idan aka ce Fulani su baro Kudu su dawo gida Arewa da zama wane tanadi aka yi masu na matsuguni da sauran bukatun rayuwarsu?”

Alhaji Ado Dansudu, ya ce “Kamata ya yi Kungiyar Dattawan Arewa da ta Afenifere ta Yarbawa da Ohaneze ta kabilar Ibo su dauki kansu a matsayin iyaye kuma dattawan kasa su rika zama bisa teburi domin tattaunawa don warware irin wadannan matsaloli su samo mafita. Amma idan suna jifar juna da miyagun abubuwa  to akwai matsala. Saboda haka batun da Farfesa Ango Abdullahi ya yi a madadin Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) kuskure ne babba.”

Dangane da zamantakewa a tsakanin Yarbawa da Hausawa da Ibo, sai Ado Dansudu ya ce, “Shekaru da yawa da suka wuce al’ummomin Arewa da Kudu maso Yamma suna amfani da wasu al’adu iri daya a tsakaninsu wadanda suka samar da cakuduwa da juna da kyakkyawar zamantakewa ta auratayya da kasuwanci a tsakaninsu. Sannan sarakunan Arewa da na Yamma da suka yi mulki a wancan lokaci sun janyo kabilun a kusa da su tare da kebe musu unguwanni aka sama musu filayen gina matsuguni da na gudanar da kasuwanci. Sai yanzu ne wadansu mutane za su fito da barazanar raba kasa wanda babban kuskure ake kokarin tafkawa.”

Ya ce, Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere ta kasa, tana da fahimtar dadadden tarihin zamantakewa a tsakanin Hausawa da Yarbawa shi ne ya sa take yin barazanar da ba za ta iya ba domin hakan ba zai taba haifar da alheri ga kowane bangare na Najeriya ba.