✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata malamai su karfafi Shugaban NAHCON – Sheikh Al’Sudani

Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini da ke Bus Stop a Hayin Malam Bello, Rigasa Kaduna  Imam Auwal Adam Al’sudani ya ce…

Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini da ke Bus Stop a Hayin Malam Bello, Rigasa Kaduna  Imam Auwal Adam Al’sudani ya ce akwai bukatar malamai su taimaka wajen karkafa wa Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), Alhaji Abdullahi Mukhtar don ya ci gaba da samun nasara wajen gudanar da ayyukansa.

Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci ofishin Daily Trust da ke a Kaduna, inda yaba wa Hukumar NAHCON a karkashin shugabancin Abdullahi Muktar kan yadda ake gudanar da aikin Hajjin bana.

“Na zo ne domin in yi kira ga malamai su karfafi Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Abdullahi Muktar saboda da shawarwarinsu yake aiki har yake samun nasarori. Su taimake shi ta wajen addu’a ba don komai ba sai don sauran jami’an gwamnati da suke rike da mukamai irin wannan su jajirce kamar yadda jajircewarsa ta sa aka samu nasara a aikin Hajjin bana kamar yadda na gani a Saudiyya,” inji shi.

Imam Sudani ya ce idan dokar kasa ta bayar da dama, ya kamata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin Shugaban Hukumar NAHCON, “Na gani da idona tun a Mina har zuwa Arafa har dawowa zuwa Makkah zuwa kwaso alhazai gida. Ni kaina lokacin dawowata ya yi amma na kara zama saboda in bai wa Alhazai gudunmawa, har na zama kamar jami’in aikin Hajji.

Babu shakka wannan abu ya sa nake ganin akwai bukatar in sanar domin amfanin sanarwar ba sai Hukumar Hajji ta Kasa kadai ba duk ma’aikatun gwamnati da ake ganin akwai sakaci da rashin tabbatar abu, idan akwai jajirtaccen shugaba kowace ma’aikata za ta iya fita daga cikin matsala,” inji shi.