✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata masu kudin Arewa su shiga gina makarantun Islamiyya da boko

Daraktan Makarantar Bin Abbas Academy da ke Unguwar Nakasari a Sakkwato, Malam Sanusi Abubakar, ya koka kan yadda jama’ar Arewa ba su kula da harkar…

Daraktan Makarantar Bin Abbas Academy da ke Unguwar Nakasari a Sakkwato, Malam Sanusi Abubakar, ya koka kan yadda jama’ar Arewa ba su kula da harkar gina makaranta ta kashin kansu, inda ya ce ya kamata masu kudin a Arewa su rika shiga sana’ar karantar da yara ilimin addini da boko a hade domin hakan zai sanya yaran su samu ingantaccen ilimi da tarbiyyar addini sabanin yadda ake yanzu.

Malam Sanusi Abubakar ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a Sakkwato, inda ya ce matsalolin da wasu jagororin kasar nan suka shiga yana da alaka da samun ilimin boko zalla da suka yi ba tare da da na addini ba.

“Mun fito da makarantar koyar da addini da boko, a shekarar 2017 a yanzu muna da dalibi 400, muna da burin samar da dalibai masu ilimi a kowane fanni da samar da mahaddata Alkur’ani mata,” inji shi.

Ya ce suna da kudirin makarantarsu ta bunkasa har su yi hadaka da wata jami’a a Najeriya ko wajenta su rika yin karatun digirin farko. Ya ce kowace rana suna ganin mafarkinsu zai tabbata yadda ake kawo musu yara ya nuna makarantar na samun daukaka da fatan  zama ta daya a Jihar Sakkwato.

“Karatun addini bai hana na boko na addini ne kan gaba duk yaron da ya haddace Alkur’ani za ka samu shi ne a gaban yaran da ba su da haddar a makaratun boko, in uba ya koyar da yaronsa Alkur’ani kasuwanci ne mai riba a Lahira, ina kiran iyaye su rika kai ’ya’yansu a makaratun da ake koyar a addini hakan zai sa ba a sace musu ruhi da tarbiyyar yaransu ba. Karatun addini na shan wahala a kasar nan don an fifita na boko samansa akwai bukatar gyara ga mu iyaye da jagororinmu.” inji Malam Sanusi Abubakar.

Ya ce, Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Sakkwato tana bayar da tallafi ga makarantu; amma ita makarantarsu ba ta taba amfana da tallafin ba, duk da hukumar ta san da zamanta. Don haka ya bukaci a duba wannan batu.