✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata mawaka su zamo masu bincike sosai – Ibrahim Kwica

Ibrahim Yusuf wanda aka fi sani da Ibrahim Kwica matashin mawaki ne kuma dan kasuwa wanda yake rera wakokin siyasa da na soyayya. A zantawarsa…

Ibrahim Yusuf wanda aka fi sani da Ibrahim Kwica matashin mawaki ne kuma dan kasuwa wanda yake rera wakokin siyasa da na soyayya. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara waka da irin kalubalen da ke ciki:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Ibrahim Yusuf. An haife ni a garin Panda da ke karamar Hukumar Albasu a Jihar Kano. A can na taso kuma na dan taba karatun addini da na boko daidai gwargado. A yanzu haka ina zaune ne a garin Kafanchan, cikin Jihar Kaduna inda nake sayar da kayan mata da gwanjo. 

Wane lokaci ka fara waka kuma me ya ja ra’ayinka zuwa ga wakar? 

Na fara yin waka ce shekara goma sha hudu da suka wuce a lokacin da wata waka ta siyasa da na yi wa wani dan takarar Majalisar Tarayya mai suna Adamu Abdu Panda wanda yanzu shi ne Ma’ajin Jam’iyyar APC ta kasa.

Abin da ya jawo ra’ayina bai wuce irin sha’awar da nake da ita kan wakokin ba. Kuma shi wannan dan siyasar ina sauraron wakokin da wadansu suke yi masa shi ne na yi tunanin to ni ma bari in gwada yi masa kuma sai Allah Ya ba ni sa’a don bayan fitowarta ta samu karbuwa sosai a wajen jama’a. 

Zuwa yanzu ka yi wakoki kamar nawa? 

Zuwa yanzu na yi wakoki masu yawa. Na siyasa kawai na fitar da wakoki sun kai ashirin. Sai na aure wadanda su kuma sun kai goma sai kuma na soyayya guda ashirin su ma. Wasu wakokin haka kawai nakan yi su yayin da wasu kuma sai an sa ni. Sai dai ba a taba amfani da wakata a fim ba, sai guda daya da aka satar min fasaha aka yi mata kwaskwarima. Da farko abin ya bata min rai har wadansu sun ba ni shawara in je in kwato hakkina amma daga baya sai na ga a matsayina na karamin mawaki hakan kamar dada tallata ni ne, shi ne ya sa ban damu ba, hasali ma dadi na ji a lokacin. 

Mene ne burinka nan gaba a harkar waka? 

Gaskiya burina shi ne in bayar da gagarumar gudunmawa a fannin fadakarwa da nishadantarwa da bunkasa adabin Hausa. Kuma ina so wata rana a rika lissafa ni cikin manyan mawakan Hausa a duniya. 

Wane alheri ka samu a dalilin waka? 

To gaskiya sanayya da mutane ma alheri ne babba, domin an ce sabo da maza jari. Na gode Allah domin wurare da dama da ban je ba, to wakokina sun je sannan ina dan samun wasu kyaututtuka da ba za a rasa ba a sanadiyyar wakar duk da ba da ita na dogara ba ina dan taba kasuwanci.

Wace matsala ka taba fuskanta a harkar waka? 

To zuwa yanzu dai babu wata matsala da na fuskanta watakila ko don babu wata waka tawa da na yi dillanci ko na bayar don yin kasuwancinta. 

Ko kana da kira ga sauran mawaka ’yan uwanka? 

Kirana ga manyan mawaka shi ne su daina girman kai a duk lokacin da wani sabon mawaki ya zo don neman shawara ko ya bukaci su taimaka su yi masa gyara ko saka muryarsu a cikin wata waka da yake son fitarwa. Su zama masu taimaka masa domin ba don ’yan koyo ba da gwanaye sun kare kuma idan kai ne yau to wata rana ba kai ba ne.

Su kuma kananan mawaka kirana gare su shi ne su rika kaskantar da kansu a gaban manyansu kuma su rika neman ilimi domin martaba sana’ar domin zamanin da ake ciki kuma a matsayinka na mai fadakarwa dole ya zama kana da ilimi kafin sakonka ya rika samun shiga. Duk lokacin da ka rubuta waka in akwai wanda ka san ya fi ka ko a fannin wakar ko a fannin kwarewa wajen sanin ka’idojin rubutu to ka kai masa ya duba ya gyara maka.

Hakazalika a fannin abin da kake son yin wakar idan wani bincike ne to ka samu kwararru ko ma’abota wannan fannin ka yi bincke mai zurfi a kai kafin ka dauki alkalami ka fara rubutu a kai. Ya kamata mawaka su zamo masu bincike sosai kan wasu fannoni da suke addabar al’umma ba kawai a kan soyayya ba. 

Ko kana da kira  ga gwamnati? 

To kirana guda daya ne kuma na san wadanda suka gabace ni a wannan jarida ta Aminiya duka sun yi irin wannan kira, wato gwamnati ta rika dafa wa mawaka saboda irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma wajen wayar musu da kai kan zaman lafiya da neman ilimi da illar zaman banza da shaye-shaye da kuma kyautata zamantakewar iyali da sauransu.