Da Dumi Dumi

Ya kashe abokinsa saboda burodi

Sufeto Janar na ‘Yan sanda Mohammed Adamu
Sufeto Janar na ’Yan sanda Mohammed Adamu

Hatsaniya ta kaure tsakanin wadansu abokai biyu Nafi’u Faruqu da Bello Muhammad, inda ta yi sanadiyar salwantar rayuwar daya daga cikinsu a Unguwar Qofar Rini da ke Qaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa a Jihar Sakkwato

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa matasan biyu aminan juna ne, inda kusan ko’ina suke tare, kuma su biyun ba su wuce shekara 24 ba kuma ba a san su da wani mugun hali ba.

“A ranar Lahadin da ta gabata ce da misalin qarfe 12:00 na dare suka yi taqaddama kan burodi a gaban gidajen iyayensu da ke Unguwar Qofar Rini, inda fada ya kaure a tsakaninsu suka riqa buge-bugen juna, kuma da Nafi’u Faruqu wanda aka fi sani da Nafi ya ga Bello wanda aka fi sani da Bellolo ya samu galaba a kansa sai ya dauko takobi ya yi masa sara uku, ya yi masa rauni aka kai shi asibiti ya rasu a can,” inji majiyar Aminiya.

Yayan marigayin Sidi Kabiru Qofar Rini, ya bayyana wa Aminiya cewa, “Na dawo gidana kafin in rufe sai Bellolo ya zo ya karbi abincinsa bayan ya fita na rufe sai na riqa jin muryoyin mutane. Da na fito ne aka fada min fada suke yi na tura qanena yayan marigayin domin ya je ya raba fadan domin abokinsa ne kuma maqwabcinmu gida biyu ne tsakaninmu da gidansu.”

“An ce ya sawo burodi ne ya ce sai ya ba shi, ya ce ba zai bayar ba, a nan ne fada ya kaure a tsakaninsu bayan an raba su. Sai Nafi ya tafi ya dauko takobi ya biyo marigayin ya sare shi a hannun dama ya sake sara masa a hannun hagu sau biyu, sai ya fadi qasa aka dauke shi zuwa Asibitin Qwararru na Jiha suka ce ba za su iya karbarsa ba a tafi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo kafin mu isa asibitin ne na kira ’yan sanda, ana cikin yi masa aiki ne minti 20 zuwa 30 Allah Ya yi naSa ikon,” inji Sidi.

ADVERTISEMENT

Ya ce bai san ko suna da wata qullalliya ba a tsakaninsu bayan rigimar burodin, kuma ya san Nafi ba ya shaye-shaye domin ko sigari ba ya sha.

Mustafa Abdullahi yayan Nafi shi ma ya ce,“Qanena ne na jini. Su kuma aminan juna ne tare suke komai, rashin fahimta ce ta shiga tsakaninsu. Bayan ya dauko makami  wani qanena ya tare shi a lokacin marigayin ya dauko gora ya buga masa shi kuma ya sare shi. Bayan jini ya buge marigayin ’yan uwansa suka ce ba su daukarsa, mu da qannenmu ya yi aika-aikar muka kai shi asibiti a can ne Allah Ya yi masa cikawa. Mun ji ciwo sosai, qaddara ce ta Allah domin kusan duk daya muke.”

’Yan sanda sun kama Nafi yana tsare a ofishinsu da ke Dadin Kowa, waqilinmu bai samu yin magana da shi ba, amma wadanda suka gan shi bayan aika-aikar sun ce ya yi nadamar abin da ya aikata.

Share