Da Dumi Dumi

Ya kashe abokinsa ya cinye marainansa

Jami’an tsaro sun kama wani mutum mai suna Mark Latunski, mai shekara 50 dan asalin Jihar  Michigan da ke Amurka, inda suke tuhumarsa da kashe wani abokinsa, bayan shirya yadda za su hadu ta hanyar na’ura, sannan ya cinye marainansa bayan kashe shi.

A rahoton kafar sadarwa ta WILD ta fitar ta ce bayanan kotun ya gano gawar wanda aka kashe tsirara mai suna Kebin Bacon, mai kimanin shekara 25 rataye a saman katakon rufin gidan Mark Latunski.

Rahoton ya ce, bayan binciken da aka gudanar an gano gawar Kebin, lokacin da jami’an suka shiga gidan Mark Latunski don binciken inda ake tsammanin ganin Kebin, a nan aka yi nasarar ganon inda aka kashe shi.

Daga bisani Mark, ya amsa laifin kisan Kebin ta hanyar daba masa wuka tare da yanka shi sannan ya yanke marainansa da wuka ya cinye.

A yanzu haka ana tuhumar Mark da laifin kisan kai da kuma cin naman mutum. An dai fara sanar da rahoton bacewar Kebin ne a ranar Kirismeti bayan bai dawo gida ba na tsawon wani lokaci.

ADVERTISEMENT

A watan Nuwamba ’yan sanda sun amsa kiran waya daga unguwar da gidan Mark yake, da ke cewa, wani saurayi mai shekara 29 ya fito daga gidan Mark a guje cikin tsoro.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya