✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe kansa saboda an doke kulob din Manchester United

Wani dan kasar Kenya mai goyon bayan kulob din Manchester United da ke Ingila ya kashe kansa jim kadan bayan kulob din Newcastle United ya…

Wani dan kasar Kenya mai goyon bayan kulob din Manchester United da ke Ingila ya kashe kansa jim kadan bayan kulob din Newcastle United ya doke na United da ci 1-0 a gasar rukunin Premier na Ingila a karshen makon jiya.
John Macharia, mai kimanin shekara 28 ya fado daga saman bene mai hawa bakwai ne a Nairobin Kenya, jim kadan bayan ’yan kwallon Manchester United sun samu rashin nasara a karo na biyu a tsakanin kwanaki hudu al’amarin da ya jefa kulob din a cikin matsala.
“John Macharia ya fado daga saman bene mai hawa bakwai ne a rukunin gidajen da ake kira Pipeline Estate bayan da kulob din Newcastle United ya doke na Manchester United a filin wasa na Old Trafford inda ya kashe kansa saboda bakin ciki”, inji Kwamandan ’yan sanda na yankin Nairobi mai suna Benson Kibui a lokacin da yake hira da ’yan jarida.
Wannan shi ne karon farko tun cikin shekarar 1972 kimanin shekara 41 da suka wuce rabon da kulob din Newcastle ya doke na Manchester a gida.
A shekarar 2009 ma an samu wani matashi mai suna Suleiman Omondi, dan kimanin shekara 29 da ke goyon bayan kulob din Arsenal da ke Ingila  ya kashe kansa jim kadan bayan kulob din Manchester United ya lallasa na Arsenal da ci 3-1 a wasa zagaye na biyu a matakin kusa da na karshe (Semi Final) a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai watau UEFA Champions League.
Kwamandan ’yan sandan yankin Nairobi Kibui ya hori matasan Kenya da su rika goya wa kungiyoyin kwallon kafa da ke kasar baya maimakon na waje saboda shawo kan matsalar yawan halaka kai da matasan kasar ke yi.