✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe kansa saboda an zarge shi da sace mazakutar matashi

Matsin lambar da aka yi wa mamacin ne ya sanya ya yanke shawarar kashe kansa.

Wani mutum mai suna Tyoakaa Tyosue, ya kashe kansa a cikin ajin wata makarantar kudi da ke kauyen Daudu a karamar Hukumar Guma ta jihar Benuwe.

Aminiya ta samu cewa mutumin ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a daren ranar Lahadin da ta gabata, bayan da ya ji matsin lamba ta zarginsa da mutanen kauyen ke yi na cewa ya sace mazakutar wani matashi a kauyen.

An gano gawar Tyosue tana reto a wani aji na makarantar Victory International da ke kauyen na Daudu, wanda tazarar tafiya ta minti 25 ke tsakaninsa da Makurdi, babban birnin Jihar.

Wani ganau mai suna Jonah, ya ce an lakaba wa mamacin satar al’aura a yayin da ya ke hanyar koma wa gida bayan ya sha giya yayi tatil.

Jonah ya ce jin haka ya sanya al’ummar kauyen suka hura masa wutar a dole sai ya dawo wa da matashin al’aurarsa, wanda zargin aikata wannan laifi da aka yi masa ba shi ne farau ba.

“Matsin lambar da aka yi wa mamacin ne ya sanya ya yanke shawarar kashe kansa,” inji Johah.

Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Catherine Anene domin jin ta bakinta, ta ce ba ta da masaniya a kan lamarin.