✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe kansa saboda budurwarsa ta guje shi

A jiya Laraba wani matashi ya kashe kansa bayan da suka sami sabani da budurwarsa wacce ta nuna masa cewa, ya nemi wata ita dan…

A jiya Laraba wani matashi ya kashe kansa bayan da suka sami sabani da budurwarsa wacce ta nuna masa cewa, ya nemi wata ita dan bata yi da shi.

Saurayin mai shekaru 25 mai suna Kehinde Muse, ya kulle kansa a dakin shi da ke unguwar Modele, a yankin Surulere sannan ya kwankwadi sinadarin guba lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, marigayin ya aike wa tsohuwar budurwar shi sakon ta wayar salula inda ya shaida mata cewa, zai sha guba ya kashe kansa tun da tace bata san shi, lamarin da ya sanya budurwar mai suna Rashidat Damilola mai shekaru 25 ta ankarar da iyayensa ta tura masu sakon da ya turo mata, nan da nan iyayensa suka nufi gidan da yake suka tarar dakinsa a rufe koda suka balle kofar suka iske shi a kwance a gado ya sha sinadarin guba yana cikin wani hali na mutuwa ko rai, nan da nan suka garzaya da shi asibiti amma kafin su isa rai ya yi halinsa kuma izuwa yanzu an kai gawarsa dakin ajiyar gawa na babban asibitin yankin domin gudanar da bincike.