Search
Subscribe
Ya kashe kansa saboda ya fadi jarrabawa

Sufeto Janar na ’Yan sanda Mohammed Adamu

Ya kashe kansa saboda ya fadi jarrabawa

Ana zargin wani matashi da ke ajin karshe a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya kashe kansa ta hanyar amfani da gubar kashe kwari. Marigayin mai suna Yunusa Aliyu wanda kafin rasuwar tasa mazaunin Unguwar Kwamba ne da ke Suleja a Jihar Neja, an gano gawarsa ce yashe a wani kango a wani yanki da ke da karancin jama’a a ranar Juma’ar makon jiya, kwana guda bayan ya fita daga gida ba tare da ya dawo ba.

Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin a ranar Talatar da ta gabata ya samu labarin cewa, wadansu mutanen unguwar ne suka sanar da ’yan sanda lamarin bayan ganin gawar tasa tare da robar maganin kwari da kuma lemon roba a kusa da ita a cikin kangon ginin da ke kusa da masaukin baki na Suleja Motel.

Bayanai sun ce marigayin wanda ke karanta darasin bi-chemistry, ya sake zaman rubuta jarrabawa a karo na 2 bayan kammala makarantar ba tare da nasara a kan darasin ba, wato “Spill ober,” amma a nan ma sai ya sake faduwa.

Wadansu da suke da kusanci da marigayin sun ce lamarin ya fusata mahaifin yaron inda a dalilin hakan ya zarge shi da sakaci  da karatu bayan ya gudanar da bincike a kan takardunsa na karatu. “Hakan ya sa ya yi masa bulala a matsayin horo da kuma jan kunne,” inji wata majiya.

Wata majiya ta ce, mahaifiyar marigayin ta rarrashi dan da kada ya dauki abin da mahaifinsa ya yi masa da zafi a zuciya, bayan ta kula da yanayinsa.

“Da farko an dauka ya dauki shawararta, kuma koda ya bar gidansu a ranar Alhamis din makon jiya an dauka ya wuce wata makaranta ce da yake koyarwa, amma sai bai dawo ba har zuwa ranar Juma’a. Bayan nan an sanar da ofishin ’yan sanda lamarin,  daga baya sai ’yan sandan suka kira iyayen yaron bayan samun labarin gano gawarsa daga wadansu jama’ar waccan unguwa,” inji majiyar.

Babban Jami’in ’Yan sandan Suleja na ‘A Dibision’, CSP Sani Zubairu wanda ya tabbatar da labarin gano gawar, ya ce sun mika gawar ga babban asibtin Suleja don tantance ta bayan gano guba da lemon kwalba na roba a kusa da ita. Aminiya ta samu labarin cewa daga bisani an binne marigayin bayan an yi masa jana’iza a yammacin ranar, bayan sallar Isha.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin