✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe mahaifinsa ya binne gawarsa

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama mutum uku ’ya’yan mutum daya da ake zargin daya daga cikinsu da kashe mahaifinsu ta hanyar tunkudo shi…

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama mutum uku ’ya’yan mutum daya da ake zargin daya daga cikinsu da kashe mahaifinsu ta hanyar tunkudo shi daga matakalar benen gidansa bayan wata gardama a tsakaninsu.

Bayan kashe mahaifin nasu mai suna Busari Isiaka mai shekara 72 sai Ibrahim Isiaka mai shekara 32 ya gayyaci ’yan uwansa suka taimaka masa wajen binne gawar mahaifin ba tare da sanar da ’yan sanda ba.

’Yan uwan uku suna daga cikin mutum 40 da ’yan sanda suka kama kan zargin aikata laifuffukan da suka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane da damfara ta hanyar tsafi da satar motoci da babura. An nuna wadanda ake zargin ne ga ’yan jarida tare da makamai da kayan tsafin da ake zargin sun yi amfani da su wajen aikata ta’asa.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu ne ya jagoranci manyan jami’ansa wajen nuna mutanen a hedkwatar ’yan sandan da ke Eleyele a Ibadan.

Da yake karin haske kan ’yan uwan uku, Kwamishinan ya ce, “Al’amarin ya auku ne a ranar 11 ga Nuwamba a Unguwar Ashi a Ibadan lokacin da gardama ta murtuke a tsakanin Ibrahim da mahaifinsa Busari a gida inda ya tunkudo mahaifin ya fado  daga matakalar benen kuma ya rasu nan take. Bayan rasuwar dattijo Busari ne, sai Ibrahim ya gayyato ’yan uwansa Taoheed Isiaka da Muritala Isiaka suka zo domin taimaka masa wajen binne gawar mahaifinsu ba tare da sanar da ’yan sanda ba.”

Ibrahim bai musanta kisan da ake zargin ya yi wa mahaifinsa ba. Su ma ’yan uwansa sun bayyana rawar da suka taka wajen taimaka wa kanensu don binne gawar mahaifinsu,” inji Kwamishinan. Sai dai Ibrahim ya shaida wa ’yan jarida cewa tsautsayi ne ya gamu da ajali domin bai yi nufin kashe mahaifinsu ba.

Kwamishinan ya kuma nuna wadansu mutum biyar masu suna Tijani Kehinde da Idowu Aliyu da Sunday Nehemiah da Rasaki Suleiman da Rafiu Kilani da aka kama su bisa zargin garkuwa da wani mai suna Abubakar Adamu a garin Eruwa. Jim kadan da samun wannan labari daga Ibrahim Abdullahi sai sassan tsaro na SARS da AKS da STS da (IRT) da hadin gwiwar mafarauta da ’yan sintiri a yankin suka fantsama cikin dajin Iyana Abeeb inda ’yan sandan suka yi nasarar kubutar da mutumin da aka yi garkuwa da shi tare da bindige daya daga cikin barayin kafin a kai ga mika musu kudin fansa.

Dukkan mutum 40 da aka kama za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike, inji Kwamishinan.