Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ya kashe matar da ta ba shi aiki don ya mallaki dukiyarta

Wani matashi mai kimanin shekaru 22 ya kashe uwwar dakin sa wacce ta dauke shi aikin share-share da goge-goge, lamarin da ya sanya mahaifiyar matar tsohuwa mai shekaru 89 ta yanke jiki ta mutu nan take

Kakakin rundunar jihar Legas DSP Bala  Elkana ya shaida wa Aminiya cewa,  jami’an rundunar ‘yan sandan sun kame matashin mai suna Joseph Ogbu dan asalin jihar Benuwe wanda matar mai suna Oreoluwa ta dauka aiki a ranar Talatar da ta gabata, “Bayan kwana daya da fara aikin sa, uwar dakin nasa ta sa shi ya yi mata goge-goge a ranar Laraba da daddare, kamar yadda ya shaida mana, a lokacin takaddama ta barke a tsakanin su, inda ya sa wuka ya soke ta nan take ta mutu, ganin haka sai mahaifiyar ta da ke gidan tsohuwa mai shekaru 89 ta yanke jiki itama ta mutu nan take, da ya tabbatar sun mutu sai ya kwashi kayayyakin su da suka hadar da wayoyin salula ya zuba a motar marigayiyar ya gudu da motar inda jami’an mu suka kama shi da ita”

ADVERTISEMENT

Ya ce, an kai gawar mamatan dakin ajiyar gawa na asibiti, kana ana  ci gaba da bincike kafin a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya.

ADVERTISEMENT