✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe mutum kan zargin kwartanci

Wani matashi mai suna Ajibade Olumuyiwa da ake zargi da hallaka wani mutum da ya ce, yana neman matarsa ce ya shiga hannun ’yan sanda…

Wani matashi mai suna Ajibade Olumuyiwa da ake zargi da hallaka wani mutum da ya ce, yana neman matarsa ce ya shiga hannun ’yan sanda a Jihar Ogun.

Matashi mai shekara 25 ya  ce, mutumin da ya kashe mai suna Olakitan Balogun yana neman matarsa ce inda yake yin lalata da ita a boye. Ya ce ya koma gida da misalin karfe 12:30 na dare inda ya iske mutumin a cikin gidansa tare da matarsa lamarin da ya sanya shi ya fusata ya yi ta dukansa ya buga kansa a jikin gini inda nan take ya mutu.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar 17 ga watan Maris din nan ne rundunar ta kama wanda ake zargin bayan da wadansu mutanen Unguwar Doland suka ankarar ’yan sandan da ke aiki a shiyyar Ajuwon cewa, wanda ake zargin ya kashe wani mutum da yake zargi da yi masa kwartanci, “Nan take muka tura jami’anmu suka kama shi a inda ake zargin ya aikata laifin,” inji shi.

Ya ce, matar mutumin mai suna Titilayo Olayiwola ta musanta zargin da mijinta ya yi wa mamacin. Ta ce, babu wata alakar badala a tsakaninsu, kuma ta ce mijin nata ya yi watsi da ita a gidan tsawon wata 8 inda ya hana ta fita ko’ina ya kuma bai wa mai gadin gidan umarnin cewa, duk lokacin da ya ga wani namiji ya shiga gidan ya ankarar da shi. Ta ce a lokacin da lamarin zai faru budurwar mamacin wanda ke yin aikin gyaran famfo ta ziyarce shi, kasancewar gidan da yake ba shi kadai ne a dakin da yake kwana ba, sai ya kawo matar gidanta inda ta ba su daki lura da alakarsu ta kut-da-kut. Ta ce ko da mai gadin ya ga mutumin sai ya kira mijinta ya sanar masa da ya zo gidan ya hau mamacin da duka ba tare da ya saurari bayanan da matarsa ko budurwar mamacin ke kokarin yi masa ba, har ya mutu.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin a tura wanda ake zargin sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar domin zurfafa bincike, inda aka ajiye gawar mamacin a dakin ajiyar gawa domin ci gaba da bincike.