✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kirkiri na’urar bude mota da fatar hannunsa

Wani mutum daga birnin  Utah da ke Amurka ya yi dashen na’urar bude mota daga jikin fatarsa, wadda take ba shi damar bude kalmar sirrin…

Wani mutum daga birnin  Utah da ke Amurka ya yi dashen na’urar bude mota daga jikin fatarsa, wadda take ba shi damar bude kalmar sirrin na’ura mai kwakwalwa tare da damar bude motarsa  ta hanyar motsi da hannunsa kusa da motar.

Mutumin mai suna Ben Workman, ya yi amfani da kimiyya wajen bai wa  na’urar  aiki yadda ya kamata bayan yin dashen ta hanyar amfani da soka wasu na’urori a cikin fatar wanda zai bada damar gudanar da ayyuka dabandaban. Kamar yadda sadarwa ta sanar KRON4.

Kafar sadarwa ta Fod13 ta wallafa rahoton cewa, Ben ya nada wasu kananan na’ukan wayoyi da suke taimakawa na’urar da ke hannunsa gudanar da ayyuka daban daban. Zai iya tashin motarsa  da bude kofofin motar a wajen aikinsa da ke lardin Probo da ke birnin Utah. Sannan yana iya kunna Kwamfutarsa ya kuma rufe ta tare da aika wasu bayanan cikin kwamfutar.

Yayin wadannan abubuwan da suke taimakawa na’urar aiki, a hannunsa na dama kuma akwai kurar karfe (maganadisu) wannan bai da bukatar ta yi aiki a matsayin wanda zata manne karfe. Kamar yadda ya bayyanawa kafar sadarwa ta Fod13.

Ben, ya ce wani lokacin yana amfani da na’urar wasu na ganin kamar abin wasa ne, ba dashen na’urar ya yi a jikinsa ba. “Ina sarrafa na’urar ne da hannuna.” Na yi kokarin amfani da ayaba, na ce masu ita ce mabudin motar, amma sai na bude motar da wannan na’urar.

Ben ya kara da cewa ya samu nasarar amfani da wannan na’urar ce ta hanyar gwaji da basirar da yake da ita amma hanyar da yabi wajen yin amfani da na’urar daga jikin fatarsa ta yi wahala sosai. Kamar yadda majiyar KRON4 ta sanar.