Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ya mutu bayan ya ci tsaka a wajen gasa

David Dowell

Wani mutum mai suna David Dowell, ya samu kwarin gwiwar cinye wata tsaka a wajen wata liyafa da aka shirya a garin Brisbane da ke kasar Austireliya inda ya mutu bayan kwana 10 da cinye tsakar.

David Dowell mai kimanin shekara 34, ya mutu ne bayan wata cutar hanji ta kama shi wadda tsakar da ya ci ta haddasa masa  kuma ya ci  tsakar ce yayin wata gasa da aka yi da shi.

ADVERTISEMENT

Iyalan David Dowell, sun yi jimamin rasuwarsa, sun kasance masu kaunarsa, kuma sun ce za su ci gaba da tuna shi a duk lokacin wata liyafa da ake shiryawa.

A cewar matar David Dowell, mai suna Allira Bricknell, ta ce ”Ba ta yin tunanin akwai wani da ya taba sanin David da zaice bai kaunarsa, saboda halayensa.“

ADVERTISEMENT

Allira Bricknell, ’yar garin Brisbane a kasar Austireliya, tana yi wa David kirari da “Jarumin mahaifin ’ya’yanta.”

“A koyaushe zan iya tuna lokacin farin ciki idan muna tare, yanzu babbar damuwata yadda zan kula da ’ya’yanmu uku, wannan babban rashi ne a gare mu,“ inji ta.

Lamarin ya faru ne a lokacin bikin Kirsimeri da ake shiryawa a gida. Ita dai Allira, ta yi alkawarin auren Dabid, tun tana da shekara 18 bayan sun hadu a wajen shakatawa da ke gabar teku, ba mu da tabbacin abin da ya kashe Dabid, kamar yadda aka rubuta a takardar shaidar mutuwarsa, ba a bayyana cewa gubar tsaka ce ta kashe shi ba, amma mu mun dauki sanadin rasuwar David Dowella haka.  Dabid ya kasance gwani wajen zane da kirkirar abubuwa.

Allira, ta kara da cewa, ”David Dowell ya kasance jarumin mutum da na taba gani a duniya kuma uba nagari ga ’ya’yanmu.”

Sai dai wani makusancin David Dowell ya gargadi sauran jama’a game da irin abin da ya faru da shi don kada ya sake faruwa nan gaba ga wani. “Kuma ina gargadin jama’a su daina kyararmu game da abin da ya faru,” inji shi.

’Yar uwar David Dowell, mai suna Hannah Dowell, ta ce dan uwanta ya rasu ne a asibiti bayan jinya. Likitoci sun yi masa gwaji cewa, yana dauke ne da wata cuta da aka gwada bayan cin wani abu, ya yi kwanaki yana fama da gudawa da ciwon ciki da zazzabi kafin ya rasu.

Jaridar Brisbane Times, ta ce ya samu matsalar ciwon huhu zuwa sauran sassan cikinsa sanadiyyar cin tsakar da ya yi.