✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu lokacin da yake lalata da wata mata a Anambra

A wannan makon ne wani tsoho mai shekara 65 a duniya ya mutu a yayin da yake tsakar lalata da wata mace mai shekaru 35…

A wannan makon ne wani tsoho mai shekara 65 a duniya ya mutu a yayin da yake tsakar lalata da wata mace mai shekaru 35 a wani otel da ke garin Awka, babban birnin kasuwanci na Jihar Anambra.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin mai suna Mista Obi Nwude da matar mai suna Ifeoma Ayinka dukkaninsu sun fito ne daga yankin Nri na Karamar Hukumar Anacha ta Jihar Anambra.

Mai Magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar, DSP Haruna Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa tun sun kame matar, kuma ana ci gaba da tsare ta a ofishinsu na B Dibison a birnin Awka inda take amsa tambayoyi. Kakakin ‘yan sandan ya ce da misalin karfe 8 na almurun ranar Juma’ar ne mahukuntan otel din suka kai rahoton al’amarin ga ‘yan sanda, kuma rundunar ba ta yi wata-wata ba ta isa wurin, karkashin jagorancin shugaban shiyyar, CSP Odian Ekeinde, inda suka tarar da mutumin kwance a kan gadon dakin otel din. Ya kuma ce an tabbatar da mutuwar mamacin ne bayan da ‘yan sandan suka ruga da shi asibiti, inda likita ya tabbatar da hakan.

A ta bakin Kakakin hukumar ’yan sandan, mahukuntan otel din sun yi zargin hakan ne yayin da matar ta zo fita daga otel din ba tare da abokin tafiyar tata ba. Saboda haka ne suka dakatar da ita domin tabbatar da cewa ko abokin tafiyar tata kalau yake, binciken da ya kai ga gano halin da ake ciki.