✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya nemi a taka wa Yuguda birki kan dage hedkwatar karamar Hukumar Tafawa balewa

dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar bogoro/Dass/Tafawa balewa a Jihar Bauchi, Barista Yakubu Dogara ya yi kira ga Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya taka…

Barista Yakubu Dogara dan Majalisar Tarayyadan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar bogoro/Dass/Tafawa balewa a Jihar Bauchi, Barista Yakubu Dogara ya yi kira ga Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya taka wa Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda birki game da dage hedkwatar karamar Hukumar Tafawa balewa zuwa garin Bununu daga garin Tafawa balewa.
Barista Yakubu Dogara ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, inda ya bukaci Shugaba Jonathan da sauran masu kaunar Najeriya, “Su matsa wa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da Gwamnan jihar, su girmama tsarin mulki ta wajen dakatar da yunkurin da ya saba wa tsarin mulki na dage hedkwatar karamar Hukumar Tafawa balewa domin kare jaririyar dimokuradiyyarmu.”  
Barista Dogara, wanda yake tare da shugabannin al’umma daga Tafawa balewa, ya ce babu dalilin da gwamnatin jihar za ta dauke hedkwatar karamar hukumar, saboda ana yawan samun tashin hankali, domin, a cewarsa, an rika samun irin wannan rikici a sassan karamar Hukumar Bauchi, inda Gwamnan ya fito, “Amma ba a yi tunanun daukar irin wannan mataki ba.”
Ya soki majalisar jihar ta Bauchi da keta tsarin mulki wajen yi wa kudirin dage hedkwatar karamar hukumar karatu na daya da na biyu da na uku a rana daya. “Kuma da wakilan majalisar suka fahimci kuskurensu, sai suka jingine kudirin, suka yi amfani da wata shawarar majalisar don dage hedkwatar karamar hukumar”. Sai ya nuna damuwa kan yadda majalisar ta dakatar da ’yar majalisar karamar hukumar, Rifkatu Samson Danna, saboda nuna rashin bin ka’ida wajen daukar wannan mataki.
Barista Dogara ya kuma soki majalsar kan yadda ta ki maida Misis Danna cikin majalisar duk da kotu ta yanke hukuncin a mayar da ita.
Ya gargadi ’yan majalisar su kasance masu bin tsarin mulki a yayin gudanar da harkokinsu, kuma su janye shawarar da suka yanke kan Misis Danna da dage hedkwatar karamar Hukumar Tafawa balewa, domin hakan ya fi karfin aikinsu.
Ya ce, bikin aza harsashin ginin sabuwar sakatariyar karamar hukumar a garin Bununu da aka yi ranar 6 ga Yuni, tsarin mulki bai san da shi ba, don haka aikin baban giwa ne.