Categories: Kurmi

Ya nemi Hukumar NDLEA ta yi masa jinyar raunin da jami’an ta suka yi masa

Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Musa Shehu Yunusari ya bukaci Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta yi masa jinyar raunin da jami’anta suka yi masa a kokon gwiwarsa shekara da suka gabata.

Alhaji Musa Shehu Yunusari, wanda ke kasuwanci a garin Fatakwal  na Jihar Ribas, ya bukaci Hukumar NDLEA din ne ta yi masa adalci kuma gwamnati ta shigo cikin al’amarin jinyar da yake fama da ita.

ADVERTISEMENT

Alhaji Yunusari ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “Kamar shekara biyu da suka wuce mun taso daga Fatakwal ni da wadansu mutanen garinmu mu uku, mun zo wani gari ana ce masa Guru sai jami’an Hukumar NDLEA suka tare mu suna binciken kayanmu. Da suka tare mu suka samu kayan daya daga cikinmu da kayan laifi wato daya daga cikin abokin tafiyarmu sai suka kama shi suka sanya masa ankwa, sai suka ce mana mu sauran fasinjojin mota mu jira sai mota ta zo muka shiga muka tafi.”

Dan kasuwar ya ci gaba da cewa, “Bayan sun tafi da yaron da suka kama can sai muka ga sun dawo tare da yaronmu, ji muke yi ma ko wani sako ne yaron zai bayar zuwa gidansu. Sai muka ji jami’an sun ce mu ma mu sauko ai duk bakinmu daya ne. Ni kuma na ce ai tafiya daya ce ta hada mu ba tare muke ba. Suka ce ai ba zai yiwu ba ai bakinmu daya ne. Bayan da muka je ofishinsu sai suka ce sai mun rubuta takardar jawabinmu na amsa cewa da saninmu tafiyarmu daya ne. Ni kuma na ce ba zan rubuta cewa da sanina ba saboda ba da sanina ba ne ba ma tafiyarmu daya ba mota ce ta hada mu.” A cewar Alhaji Musa Yunsari, sai wani jami’in Hukumar NDLEA din “Ya dauko sanda ya tilasta min a kan sai lallai in ce da sanina ne, ni kuma na ce ban sani ba, sai ya rika dukana da sandar.”

ADVERTISEMENT

Dan kasuwar ya ce, sakamakon dukan da aka yi masa ya ji mummunan rauni. “Sun doke ni a kan kokon gwiwa sanadin dukan da aka yi mini a wurin ko yawo ba na iyayi, na je asibitoci da dama na je asibitin Damaturu na je na Guru har Asibitin Gashuwa na je duk bai yiwu ba daga nan na tafi Asibitin Kashi na Kasa da ke Dala a Jihar Kano. Wani babban lilkita da ya duba sai ya ce wannan abin sakamakonsa abin da ya nuna wannan kokon gwiwar ne ya rabe biyu, don haka sai dai a yi mini aiki,” inji shi.

Ya baiyana lamarin da abin takaici da  rashin iya aiki. Ya kara da cewa, idan da akwai kwarewa a aiki tunda an samu mai laifi sai a tafi da shi maimakon tursasaw a wanda bai ji ba bai  gani ba kan ya amsa laifin da bai aikata ba har ma a yi masa rauni .

Kuma saboda jinyar da yake yi sanadiyyar wancan cin zarafi, iyalansa na cikin wani hali na bukatar taimako na musamman.

Ya ce zuwa yanzu ya kashe kudi domin neman lafiyarsa sama da Naira dubu 500 kuma ana bukatar wasu Naira dubu 300  domin yi masa aiki a Asibitin Kashi na Dala da ke Kano.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin jami’an Hukumar  NDLEA da ya yi  zargi da sun ci zarafinsa ya ci tura.

..

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago