✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya saba wa ka’ida a ba Jonathan tikitin takara kai-tsaye – Kuit

Shugaban Jam’iyyar PDP ta Jihar Jigawa Alhaji Salisu Mahmuda Kuit ya ce ba Shugaba Jonathan tikitin takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa kai-tsaye ba…

Shugaban Jam’iyyar PDP ta Jihar Jigawa Alhaji Salisu Mahmuda Kuit ya ce ba Shugaba Jonathan tikitin takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa kai-tsaye ba tare da barin wakilan jam’iyya su fafata a zabe ba, ya saba wa tsarin mulkin Jam’iyyar PDP.
Alhaji Salisu Mahamuda Kuit ya fadi haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse dangane da rade-radin uwar jam’iyyar ta kasa za ta turo kantoman riko jam’iyyar a Jihar Jigawa saboda wai a ganin jam’iyyar suna shugabantarta ne ba bisa ka’idar ba.
Ya ce shugabancin jam’iyyar na kasa ya yi kadan ya ba Shugaba Jonathan damar tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2015, saboda yin hakan ya saba wa ka’idar jam’iyyarsu ta PDP.
Game da batun mika jam’iyyar a hannu Alhaji Saminu Turaki da aka ce uwar jam’iyyar shirin yi, ya ce hakan ya saba wa ka’ida domin su zabarsu aka yi kuma babu dalilin da zai sa a rushe shugabancinsu ba tare da wasu dalilai ba.
Ya ce Saminu ba dan jam’iyyarsu ba ne, kuma duk da cewa an ce ana ganinsa a tarurrukan da uwar jam’iyyar ke yi hakan bai isa ba, dole sai Saminu ya koma mazabarsa ya sake sabunta katin rijistarsa na dan jam’iyya domin a baya ya koma ACN.
Ya ce batun turo kantoma domin jagoranta jam’iyyar bai taso ba domin babu hurumin da ya ba da damar a ce uwar jam’iyyar ta turo kantoma alhali ba gazawa suka yi ba domin kowa ya sani suna tare da Jam’iyyar PDP a sama babu wata matsala tsakaninsu da jam’iyyar ta kasa ba su kuma da wata matsala da Gwamnatin Tarayya.