✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya sanya riguna 15 a jikinsa don kauce wa biyan kudin dakon kaya a jirgin sama

Wani fasinja mai suna John Irbine, daga kasar Scotland da ya fahimci cewa, kayansa ya wuce adadin nauyin da ake bukata ya yanke shawarar bullo…

Wani fasinja mai suna John Irbine, daga kasar Scotland da ya fahimci cewa, kayansa ya wuce adadin nauyin da ake bukata ya yanke shawarar bullo da sabuwar dabarar kauce wa biyan kudin dako a jirgin saman da zai shiga, bayan da jakar kayansa ta kai nauyin kilo takwas kuma ba za a  bar shi ya shiga cikin jirgin ba, har sai an gwada nauyin kayansa bayan gwajin zai biya wasu karin kudi.

Sai John Irbine, ya sanya rigunan da suka kai nauyin kilo a jikinsa. Saboda a cewarsa biyan wannan kudin dakon kayan jirgin zai iya zamar masa wani asarar kudi.

Iyalan John Irbine, sun jima suna yin tafiye-tafiye daga garin Nice a kasar Faransa zuwa filin jirgin saman Edinburgh na Ingila. Dan John Irbine, mai suna Josh ne ya wallafa hakan a shafinsa na Tiwita, lokacin da mahaifin nasa yake sanya rigunan masu nauyin kilo takwas yana zufa. Josh, mai shekara 17 kamar yadda kafar sadarwa ta Metro.co.uk ta ruwaito, ya kara da cewa, a hanyarmu ta dawowa gida Bearsden, Glasgow daga Faransa a daren ranar Asabar, ba mu taba tsammanin cewa, za mu shiga jirgin sama ba tare da an ce mu kara kudin dakon kaya ba, saboda kayan da muka dauka ya wuce nauyin kilo takwas da za a iya barinmu mu shiga jirgin ba mu biya karin kudi ba.

Josh, ya ce lokacin da mahaifina, zai shiga jirgin jami’an jirgin sun tambaye shi ko zai biya karin kudi ne, ganin kayan da yake da su. Sai ya ce a’a, kawai sai ya bude jakarsa ya fara ciro rigunan da suka kai 15 yana sakawa a jikinsa don rage yawann nauyin kayan da ya dauko. Hakan ya sa na rika yi masa dariya. Jami’an tsaron filin jirgin saman sun yi tunanin John, zai yi safarar wasu abubuwa ne a jikinsa, amma bayan kammala bincike sai aka fahimci kawai ya yi hakan ne don rage nauyin kayan da ya dauka kuma da shirin kada ya biya kudin dakon kayan.