✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya shawarci shugabanni da ’yan Arewa mazauna Kudu

Shugaban ’yan Arewa mazauna garin Benin a Jihar Edo Alhaji Badamasi Saleh ya shawarci shugabannin ’yan Arewa mazauna Kudu da suka hada da ’yan siyasa…

Shugaban ’yan Arewa mazauna garin Benin a Jihar Edo Alhaji Badamasi Saleh ya shawarci shugabannin ’yan Arewa mazauna Kudu da suka hada da ’yan siyasa da malaman addinin Musulunci da na Kirista su tashi tsaye wajen fadakarwa da hada kan jama’a.
Alhaji Badamasi Saleh ya bayyana haka ne a cikin zantawarsa da Aminiya a Benin, inda ya ce rashin hadin kai da son zuciya na hana zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Ya shawarci shugabannin al’umma musamman na ’yan Arewa mazauna Kudu su kasance masu adalci ga jama’arsu kuma su kusanci wadanda suke jagoranta domin gane matsalolinsu da sauraron koke-kokensu.
Shugaba Badamasi ya soki ’yan siyasa masu hana ruwa gudu a kasar nan ya ce  “Kowa ya san duk wata fitina da ke tasowa a kasar nan salsalarta daga bara gurbin ’yan siyasa ne da ke gurbata tarbiyyar matasa ta ba su kayan maye lokacin kamfe da zabe. Sai ya yi kira ga matasa su fahimci cewa lokaci ya yi da za su dawo daga rakiyar irin wadannan marasa kishin kasa da suke ingiza su ga halaka, yayin da suke kai ’ya’yansu kasashen Turai suna karatu idan sun dawo su mai da su tamkar bayinsu.
Alhaji Badamasi Saleh ya yaba wa Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo kan yadda take tafiyar da aikinta ba sani ba sabo wajen tabbatar da tsaro a jihar.