✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya taimaka an yi wa bakin mahaifinsa fashi

Wani matashi mai suna Abdu Rabi’u da ke zaune a garin Idiroko a Jihar Ogun ya furta da bakinsa cewa shi ne yake bayar da…

Wani matashi mai suna Abdu Rabi’u da ke zaune a garin Idiroko a Jihar Ogun ya furta da bakinsa cewa shi ne yake bayar da labari a boye ga wadansu ’yan fashi da makami suke bin sawun mutanen da suka yi canjin kudade a ofishin mahaifinsa suna kwace musu kudaden bayan sun nuna musu bindiga.
Audu Rabi’u, mai shekaru 33, wanda ya kammala karatun digirinsa a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) a shekarar 2012, ya ce an haife shi ne a kasar Ghana, amma ya yi karatun firamare da sakandare a garin Idiroko, wato garin da mahaifinsa yake zaune da iyalinsa yana hada-hadar canjin kudade.
 Da yake nuna wa manema labarai wadansu ’yan fashi su 7 har da Audu Rabi’u a cikinsu a ofishinsa a garin Abeokuta ranar Talatar makon jiya, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Ogun, Mista Ikemefuna Okoye ya ce an kama Rabi’u ne a dalilin bayanan da abokansa suka yi cewa yana da hannu a cikin ayyukan nasu da suka yi a baya. Kwamandan rundunar yaki da fashi da makami (SARS) ta Jihar Ogun, SP Mohammed Tijjani shi ne ya jagoranci jami’ansa da suka yi nasarar kama wadannan barayi a ranar 8 ga wata Maris a wata maboyar shaye-shaye da ke mararrabar Ilogbo a garin Ifo. Kwamishinan ya  ce an kama su ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar, a daidai lokacin da suke shirin kai hari a wani gidan sayar da mai, kuma an samu manyan bindigogi guda 4 da harsasai guda 25 a tare da su.  Sunayen ’yan fashin, kamar yadda Kwamishinan ya bayyana, su ne Adesanya Emmanuel da Olukutan Ibrahim da Saheed Nureni da Opeoluwa Sese da Eyitayo Bolarinwa da Oyedele Peter da kuma Yomi Akinola, wadanda suka ambaci sunan Audu Rabi’u da aka kama shi daga baya. Kuma dukkansu ba su musanta irin danyen aikin da suka yi a baya ba.
 Wakilinmu ya samu tattaunawa da  Audu Rabi’u, wanda ya bayyana cewa, “A cikin shekarar 2012 na kammala karatun digiri na fannin Archeology a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Na yi aikin bautar kasa a Jihar Binuwai a shekarar 2013, daga nan sai na dawo garin Idiroko. Na sayi motar da nake amfani da ita wajen dakon buhunan shinkafa da ake yin fasa kwaurinsu. Wadannan yara (’yan fashi) da ka ganni tare da su, a gaskiya, ni ne nake ba su labarin cewa akwai baki a tare da ni wadanda suka yi canjin kudi su je su tare su a hanya su kwace kudaden kafin a fita da su. Na farko da muka yi, mun yi nasarar kwace Sefa miliyan 5 (daidai da Naira miliyan 1 da dubu dari 7 da 75), inda aka ba ni Naira dubu dari 3 a matsayin nawa kason. Na biyu an kwace Sefa dubu dari 2, amm ban samu ko kwabo ba. Haka ma na uku da na hudu da suka kwace Sefa miliyan 20 (kusan Naira miliyan 6), alkawari kawai suka yi, ba tare sun ba ni komai ba. Sau daya kawai na taba samun nawa kason.”
Da aka tambaye shi yadda suka hadu da sauran matasan ’yan fashin, sai ya ce, “Duk wadannan yara babu wanda na sani a cikinsu, ainihin abokin nawa mai suna Taiye, wanda ya gudu ba a gano shi ba tukuna, shi ne ya hada ni da direban da ke tuka motar da ake amfani da ita. A matsayinshi na abokina Taiye, shi ne ya tuntube ni cewa yana so shi ma ya fara sana’ar canjin kudade, na gaya masa cewa sai ya samo kamar Naira dubu 750 sannan ne zan nuna masa yadda zai shiga cikin sana’ar canjin kudi, inda a nan take ya fito da Naira dubu 150  har ya ba ni kyautar Naira dubu 15 daga ciki. Daga wannan lokaci ne ya fara neman sanin yadda zan nuna masa abokanan mahaifina da suke tafiye-tafiye da kudaden Sefa a hannunsu, amma ban ba shi fuska ba. Ni ban san abun da ya kai ni ga amincewa da hakan ba, aikin shaidan ne.
 “ A cikin watan Satumba na bara ne na fara hulda da wadannan mutane, inda muke kwace kudade daga hannun mutanen da suka yi canji daga wurin mahaifina. Na jefa kaina cikin wannan matsala ne domin ina matukar bukatar kudin da zan samu shiga aikin kwastam. Duk abun da uba yake yi wa dansa mahaifina ya yi mini, domin ya dade yana daukar dawainiyata, babu abun da na rasa. Ni da kaina na yi takaicin jefa kaina cikin wannan hali, domin idan ma an sallame ni daga hannun jami’an tsaro da suka kama ni,  na san cewa ba zan gama da duniya lafiya ba domin kalaman tsinuwa da ke yawan fitowa daga bakin mahaifin nawa. Na san fushi ne ya sa shi yake tsine mini, kuma ka san yadda matsayin tsinuwa take a tsakanin da da mahaifi.” Inji Abdu.
 Shi kuwa direban da ke tuka motar da suke amfani da ita, mai suna Olukutan Ibrahim, cewa ya yi, “Sau uku ina tuka motar da muke zuwa yin fashi da makami da ita. A karo na farko an ba ni kaso na Naira dubu 150, na biyu kuma na samu Naira dubu dari daya, sai na uku da na tashi da Naira dubu 20 kawai. Na yi amfani da kudin ne wajen biyan wadansu bukatuna.”
Shi kuwa Peter Oyedele cewa ya yi, “Har yanzu ba a gano jagoran tawagar tamu ba, domin ya tsere, shi ne yake tsara yadda za mu fita yin aiki da ainihin wurin da za mu je. Idan mun kammala aikin sai ya ba kowa nasa kason. Sau 4 ana fita aiki da ni, kuma an ba ni kason Sefa dubu dari 3 a karo na farko, na biyu na samu Sefa dubu 50, sai na uku da na tashi da Sefa dubu 30, a na hudu kuma na tsira da Sefa dubu dari 7. Na yi amfani da kudin ne wajen sayen wannan motar da aka kama ni da ita.”
 Wakilinmu ya je Idiroko da ke kan iyakar Najeriya da kasar Benin, inda ya ji ta bakin Alhaji Abdullahi Musa dangane da kama babban dansa Rabi’u kan zargin yana bayar da labari a boye ga ’yan fashi da makami da suke kwace kudade daga hannun mutanen da suka yi canji a hannunsa. s
Alhaji Abdullahi Musa, wanda ake yi wa lakani da Audu Biri ya ce, “Wallahi Tallahi ni dai ban taba tunanin wannan yaro zai aikata irin wannan mummunan abu ba, domin yaro ne matashi mai kwazo da fafutukar neman abun da zai dogara da shi ba tare da ya jira ya samu daga gare ni ba. Ni ne na saya masa motar da yake amfani da ita domin ya dogara da kansa. A can baya jami’an tsaro sun taba kama shi suka kai shi Adeniji Adele da Panti CID a Legas, amma bayan sun kammala bincike suka sallame shi, domin an gano cewa makirci ne aka kulla masa. Saboda haka a lokacin da na fara samun wannan labari  ban amince ba, domin ina ganin cewa wadanda suka sanya masa ido ne suka sake kulla makircin nasu. Ni dai na bar komai ga Allah (SWT).”