✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yanke kansa wajen bikin Ashura a Indiya

Wani dan Shi’a a kasar Indiya ya gille kansa bisa kuskure lokacin makokin Ashura da ya gabata. Mutumin mai suna Mohammed Sayum, ya yi kuskuren…

Wani dan Shi’a a kasar Indiya ya gille kansa bisa kuskure lokacin makokin Ashura da ya gabata.

Mutumin mai suna Mohammed Sayum, ya yi kuskuren yanke kansa ne lokacin da yake nuna bajinta ta hanyar wasa da takobi a garin Nalanda da ke Gundumar Bihar a gabashin Indiya.

Rahotannin da kafafen watsa labaran kasar sun ce, Mohammed Sayum mai shekara 60 ya yi kuskuren yanke kansa ne, inda nan take aka nufi Asibitin Sadar da shi, sai dai ya rasu  a hanyar zuwa asibitin sanadiyyar zubar da jini da yake yi.

Wannan kuskure ya janyo jimami a yankin kamar yadda kafar labarai ta Swarajya ta wallafa.  Daruruwan mabiya Shi’a kan yi amfani da takwabi wajen nuna bajintarsu don nuna  alhini kan kisan Imam Husain lokacin yaki Karbala a karni na farko na Musulunci.

Dan marigayin mai suna Feroz, ya bayyana wa ’yan sanda cewa, yana wurin lokacin da abin ya faru.

A yanzu haka ’yan sandan Bihar, suna ci gaba da bincike kan gawar marigayi Mohammed Sayum.

Mabiya Shi’a suna amfani da ranar Ashura da kuma kusan daukacin watan Muharram a matsayin lokacin jimamin rasuwar Imam Husain bn Ali, jikan Manzon Allah (SAW), wanda shi ne na uku a jerin Imaman Shi’a. Imam Husaini dai ya hadu da ajalinsa ne a fafatawar Karbala lokacin da sojojin Yazid suka kashe a shekarar 680 Miladiyya.

Mabiya Shi’a suna gudanar da abubuwa da dama don tuna wannan rana da suka hada da ziyarar Karbala  da ke kasar Iraki. Kuma suna tattaki a a kasashe da dama, yayin da wadansu suke kunna wuta, wadansu kuma su rika dukan jikinsu ko yanka jikinsu da wuka ko takwabi har sai jini ya fita. Saura kuma sukan rika dukan kirjinsu da marin fuskarsu.

Akan samu hadurra da dama a lokutan zagayowar wannan rana a wuraren da mabiya Shi’a suke, kuma irin hakan ne ko a ranar Talatar makon jiya akalla mutum 31 sun mutu  lokacin bikin tunawa da wannan rana sakamakon turmutsetseniyar da aka samu lokacin jerin gwanon Karbala yayin da aka raunata sama da mutum 100. Kamfanin Dillancin Labarai na  AP ya wallafa cewa ana zubar da jini  lokacin da ake irin wannan tattaki.

Har wa yau a ranar Ashurar mutum 20 sun samu raunuka lokacin da suke kallon masu faretin tunawa da ranar a  garin Andhra Pradesh a Kudancin Indiya, inda rumfar da suke ciki ta auka musu da misalin karfe 2:00 na dare. A rahoton da ’yan sandan yankin suka fitar ya ce, rumfar ta fado musu ne a daidai lokacin da suke kallon masu  fareti na Pedda Saragathi suna taka garwashin wuta don nuna jimamin ranar Ashura.

A makon ranar Ashura a Jihar Uttar Pradesh wutar lantarki ta ji wa wani mutum rauni lokacin da ’yan Shi’ar suke bikin ranar Ashura lokacin da suka rike da wayoyin lantarki.

Rahotanni sun bayyana cewa, akalla mutum hudu sun mutu a Karachi na kasar Pakistan sanadiyyar amfani da wayar wutar lantarki lamarin a ranar Asabar a garin Bhittaiabad da suke makwabtaka da garin Gulistan-e-Jauhar.

A shekarar 2004 an samu tashin bam a garin Karbala da Baghdad ranar Ashura inda mutum 140 suka rasu.