Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ya yi shekara 40 ba tare da yin aski ba

Sakal Dev Tuddu
Sakal Dev Tuddu

Wani tsoho mai shekara 63, mai suna Sakal Deb Tuddu dan kasar Indiya ya shafe shekara 40 bai yi aski ko wanke kansa ba, hakan ya sa sumarsa ta yi tsawo sosai wani lokaci yakan daure sumar kamar rawani, a haka yake ta yawo da ita.

Sakal, haifaffen kauyen Mandada a Jihar Bihar da ke gabashin Indiya, ya bayyana cewa ya ki yin aski ne tun yana shekara 22 saboda wasu dalilai.

ADVERTISEMENT

Ya ce wata rana ya tashi da safe sai ya fahimci cewa sumar duk ta daddaure saboda rashin aski da kuma wankewa.

Sakal, ya dauki wannan matakin kin aski a matsayin wata karama daga abin bautarsa na Hindu mai suna ‘Shiba’ tun daga wancan lokaci da ya fahimci cewa akwai wannan karamar sai ya yanke shawarar daina yin aski da wanke kansa.

ADVERTISEMENT

A yanzu tunda har sumar ta yi tsawon zai iya daure ta, sai ya yanke shawarar ya ci gaba da nade sumar tamkar rawani, wani lokaci idan zai fita daga gida sai ya yi amfani da farin rawani don rufe sumar saboda daudar da ta yi.

A lokacin da Sakal, ya daina aski sai aka fara yi masa lakabi da ‘Mahatma Ji’ musamman jama’ar Mandada a wani sunan girma da za a iya karramawa.

Jama’ar Mandada suna karrama shi, shi kuma yana ganin yana da wata baiwa ce don haka jama’a daga sassan garuruwan Indiya ke zuwa wajensa don samun waraka musamman magungunan gargajiya.

Sakal, dai ba shi ne  dan kasar Indiya na farko da ya yi shekaru bai yi aski ba. Shekara uku da suka wuce an samu rahoton wani mai suna Sabjibhai Rathwa, dan garin Gujarat da ya bar sumarsa har ta yi tsawon mita 19 ba tare da yin aski ba.