✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi wa budurwa fyade bayan ya zuba ma ta wiwi a abinci

Wani matashi mai suna Innocent Ifunayachi mai shekaru 34 ya yaudari budurwa ‘yar shekaru 14 inda ya sanya ma ta garin tabar wiwi a indomi,…

Wani matashi mai suna Innocent Ifunayachi mai shekaru 34 ya yaudari budurwa ‘yar shekaru 14 inda ya sanya ma ta garin tabar wiwi a indomi, bata fargaba taci ta fita hayyacin ta anan ya yi mata fyade.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Larabar da ta gabata ne dangin yarinyar suka shigar da kara a ofishin rundunar ‘yan sandan da ke Bariga a Legas lamarin da ya kai ga kame matashi.

Ya ce, matashin yakan ziyarci dangin yarinyar, kana a lokacin da zai yi aika-aikar ya ziyarci gidan kamar yadda ya saba ko da yaje ya iske yarinyar ta tasa abinci a gaba zata ci sai da ta tashi domin ta debo masa ruwa ya sha kafin ta dawo ya barbada mata garin tabar wiwi ko da taci abincin ta fita hayyacin ta sai ya yi lalata da ita.

DSP Bala Elkana, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa za kuma a gurfanar da shi a gaban kotu yayin da aka kai yarinyar asibiti domin bincikar lafiyar ta.

Daya daga cikin wadanda ake zargin

Haka zalika Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar Larabar ofishin ‘yan sandan da ke Bariga ya samu koken wasu iyali da suka ce wasu gugun matasa sun yi wa ‘yar su mai shekaru 13 fyade kuma har ta dau ciki.

Ya ce, wadanda ake zargin sun hadar da Kazeem Bello mai shekaru 26 da Dayo A Maker dan shekaru 24 dukan su na zaune ne a Unguwar Elaje a yankin Bariga, wadanda ake zargi da sun hadu suka yi wa yarinyar ‘yar shekara 13 fyade kuma a sanadin haka ne ta haifi ‘ya mace makwanni 5 da suka gabata, ya ce  wanda ake zargin sun yi barazanar kashe yayrinyar idan ta bayyana abin da ya faru, sai dai ta sami kwarin gwiwar fadawa iyayen ta ne bayan da waxanda ake zargin suka yi yunkurin yi wa kanwarta fyade.

DSP Bala Elkana, ya ce an kama daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Dayo yayin da dayan ya ranta a na kare inda rundunar ta bayar da sanarwar lalubo shi.