✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi yunkurin halaka abokin huldarsa kan Naira 10

Wani mutum da ke sayar da kayan masarufi a unguwar Idimu da ke Jihar Legas mai suna Musa Umaru ya bayyana yadda wani abokin huldarsa…

Malam Musa Umaru da raunukan da aka yi masaWani mutum da ke sayar da kayan masarufi a unguwar Idimu da ke Jihar Legas mai suna Musa Umaru ya bayyana yadda wani abokin huldarsa ya yi masa rauni da wuka a kan ya tambaye shi bashin da yake binsa na Naira 10 da ya sayi taba a wurinsa.
Malam Musa, wanda ake yi wa lakabi da Maitaba, ya bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya kai su ga zuwa kotu inda suke tafka shari’a.
Ya ce, “Kunle yakan karbi kayana bashi, amma da na fahimci ba ya son biyan bashi, sai na daina ba shi kayana domin duk lokacin da na tambaye shi kudina, sai ya rika yi min barazanar sai ya ci mutuncina. Ran nan ya zo shagona ya bukaci na bashi tabar Naira 10 sai na ki ba shi, sai kawai ya sa hannu ya dauki taba guda daya ya kunna a gabana ya shanye, ya ce kuma ba zai biya ni ba, ni kuwa na ce dole sai ya biya ni kudina. Muna cikin cacar baki, sai kawai ya fito da wuka ya rika caka mini. Cikin kankanen lokaci ya yi mini kaca-kaca da rauni, jini ya rika zuba ta ko’ina a jikina, daga nan ban san yadda aka yi ba, sai kawai ganina na yi a kan gadon asibiti. Daga bisani sai muka yanke shawarar kai shi kara wurin ’yan sanda daga nan kuma aka kai mu kotu yanzu har an dage shari’a zuwa wani lokaci”.
Kunle ya ki cewa uffan lokacin da Aminiya ta tuntube shi, amma lokocin da aka gurfanar da shi a kotun gargajiya da ke Idimu, Kunle Oyebanji ya karyata zargin da ke yi masa na yi wa Musa rauni da wuka, amma bai musanta karbar bashin taba ba kuma bai musanta yin fada da Musa ba.
Alkalin kotun, Mai shari’a Mista P.E. Nwaka ya ba da belin Kunle a kan Naira dubu 50 tare da shaidu guda biyu da suka mallaki adadin kudin, daga bisani ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga wannan wata na Agusta.