✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya zama wajibi mu kawo karshen kalaman kiyayya-Osinbajo

  Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya ce ya zama wajibi kada a bari wasu su rika fakewa da ’yancin fadar albarkacin baki suna yada…

 
Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya ce ya zama wajibi kada a bari wasu su rika fakewa da ’yancin fadar albarkacin baki suna yada kalaman kiyayya a tsakanin ’yan Nijeriya.
Osinbajo ya yi furucin ne a taron karawa juna sani kan hadin kan kasa da Cibiyar Nazarin Tsaro ta shirya a Abuja, a jiya.
“Ya zama wajibi mu takaita tare da dagewa a kan cewa mutane ba su rika yin kalaman da za su haifar da tashin hankali ba”. Inji shi
Ya bayyana cewa kalaman kiyayya su ne suka haifar da mafiyawan rikice-rikicen da suka faru a tarihi.
Ya kara da cewa masu yada muggan kalaman sau da yawa sukan yi amfani da kafafen yada labarai musamman kafafen sa-da-zumunta don cimma manufarsu.
Ya yi Alla-wadai da karairayin da masu son wargaza kasar nan ke yadawa na batanci.
Ya ce daya daga cikin karairayin su ne wai duk kasar da ta kafu ta yadda aka kafa Nijeriya to dole ta ruguje.
Ya bayyana cewa misalin da suke kawo wa karya ne domin kasashe da yawa sun kafu ne saboda wasu dalilai na tarihi kawai ba ta hanyar amincewar jama’arsu ba.