✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya zargi ’yan takarar APC da kasancewa ’yan kungiyar asiri

Gwamnan Jihar Bayelsa Mista Seriake Dickson ya zargi dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC a zaben Gwamna da za a yi ranar 16…

Gwamnan Jihar Bayelsa Mista Seriake Dickson ya zargi dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC a zaben Gwamna da za a yi ranar 16 ga Nuwamba da cewa dan kungiyar asiri ne kuma dan ta’adda. Gwamnan ya yi wannan  zargi ne a ranar Talata lokacin da yake kaddamar da ayarin masu yi wa Jam’iyyar PDP yakin neman zabe a sakatariyar jam’iyyar da ke Yenagoa babban birnin jihar.

Gwamna Dickson ya ce dan takarar Jam’iyyar APC, Mista Lyon da Mataiakinsa Mista Degi gayyar ’yan ta’adda ne da kungiyar asiri da sauran miyagun ayyuka. Gwamnan ya ce babu wani abin a-zo-a gani da gwamnatin APC ta tsinana wa kasar da kuma jihar a tsawon shekara biyar tana mulki in ban da haddasa tashe-tashen hankali da ayyukan ta’addanci da tsageranci da fadace-fadace.

Daga nan ya sha alwashin ba za su taba bari, tsageranci da ta’addanci su samun wurin zama a Jihar Bayelsa ba a karkashin mulkin dimokuradiyya domin haka ba za su taba bari APC ta kafa gwamnati a jihar ba idan kuwa har hakan ta kasance suka sake ta kwace mulki al’ummmar jihar za su shiga uku.

Ya kara da cewa “Idan kuka bari aka zabi mutanen can suka hau mulki, to babu sauran wani dan jihar nan da zai sakata ya wala, dole kowa ya bar jihar matukar yana son ya zauna lafiya domin ’yan ta’adda sun karbi jagorancin jihar.”

Daga nan sai ya gargadi al’ummar jihar da kada su sake a yi musu sakiyar da babu ruwa idan kuwa suka yi wasa aka fadi zabe to su tabbata washegari 17 ga Nuwamba kowa ya tattara ’yan komatsensa ya san inda dare ya yi masa domin gwamnati mai cike da hadari ta shigo mulki, inji Dickson.