✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaba Kyauta: An karawa sojan da ya tsinci Naira Miliyan 15 girma

Shugaban rundunar Sojin saman Najeriya Abubakar Sadik, ya tabbatar da karawa jami’in Sojin Saman Najeriya (ACM) Bashir Umar, girma wanda ya tsinci makudan kudi Yuro…

Shugaban rundunar Sojin saman Najeriya Abubakar Sadik, ya tabbatar da karawa jami’in Sojin Saman Najeriya (ACM) Bashir Umar, girma wanda ya tsinci makudan kudi Yuro dubu 37 (£37,000) daidai da Naira miliyan 15 kuma ya mayar ga mai shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Shugaban ya yi wa Bashir karin girman ne a Hedkwatar sojin saman Najeriya da ke Abuja a jiya lokacin da aka shirya liyafa ta musamman a matsayin yaba kyauta.

An karawa matashin matsayi zuwa Kofur (Corporal) a matsayin tukwaicin abin alhari da ya yi.